A ‘yan kwanakin nan dai, Nijeriya ta tsinci kanta a cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar karancin takardun kudi na naira, wanda idan ba a tsaya an kula yadda ya kamata ba, akwai barazana ga zaman lafiya da ci gaban al’ummar wannan kasa.
Ko shakka babu, wannan lamari ya yi fice a cikin na’urorin ATM da POS da kuma bankunan wannan kasa, wanda ya haifar da damuwa a tsakanin talakawan baki-daya. Matsalolin da ke tattare da wannan karanci na takardun kudi, na da matukar yawan gaske; sannan kuma suna haifar da babbar barazana ga tattalin arziki da kuma yin tasiri ga rayuwar yau da kullum na ‘yan Nijeriya.
- CAC Ta Bayyana Dalilan Da Ke Kawo Durkushewar Kamfanoni A Nijeriya
- Bashin Cikin Gida Ya Karu Da Kashi 134, Ya Kai Naira Tiriliyan 52
Matsalar tabarbarewar rashin tsabar kudin dai, ta samo asali ce sakamakon wasu dalilai da suka hada da matakan da gwamnati ta dauka na cire tallafin man fetur da faduwar darajar naira a kasuwar canji da makudan kudaden shiga wanda gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi ke samu ta hanyar karbar kasafin kudadensu na kasa (FAAC), kazalika wani abu mafi muhimmanci shi ne; rashin sanin makamar aiki da kulawa da tsarin kudi na Nijeriya.
Mece Ce Illar Da Al’umma Ke Fuskanta?
Na’urar ATM na bushewa a fadin kasar nan, wanda hakan ke haifar da takaici tare da rashin tabbas a tsakanin ‘yan Nijeriya. Wannan karanci, ba wai kawai yana kawo cikas ga hada-hadar yau da kullun ba ne kadai, har ma yana haifar damuwa game da karfin tattalin arziki wannan kasa.
- Akwai hatsari ga talakawan Nijeriya, sakamakon karancin kudi na zahiri yana da matukar nauyi, musamman ga ‘yan kasar da suka dogara da hada-hadar kudi; domin bukatunsu na yau da kullun. Alal misali, kamar kananan ‘yan kasuwa, masu sayar da abinci, masu tura baro da kuma wadanda ba su da tsarin biyan kudi na zamani da sauran makamantansu. Haka zalika, tabarbarewar kudi; na kara ta’azzara kalubalen tattalin arzikin da ake ciki ba tare da samun kudin ba, saboda haka ta yaya za su ciyar da iyalansu da ‘yan’uwa na kusa da na nesa?
III. Haka nan kudaden da ake caja na POS, wani nauyi ne a kan ‘yan Nijeriya, sakamakon karuwar kudaden da ake kashewa ta hanyar mu’amalar na’urar POS din na karuwa. Wannan ci gaban, yana sanya karin damuwa a aljihun mutanen da suke kokawa a kan matsalar hauhawar farashi.
- IB. Cire tallafin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki, wani bangare ne na tushen wannan tabarbarewar rashin takardar kudi, sannan kuma suna da alaka da manyan batutuwan tattalin arziki.
Har ila yau, cire tallafin man fetur din ya haifar da hauhawar farashin sufuri, wanda kuma ya haifar da tasiri a sassa daban-daban. Sakamakon hauhawar farashin kayayyakin; ya sa kayayyakin da ayyuka sun yi tsada, inda ya kara fitar da kudade daga aljihun talakawan Nijeriya.
- B. Zurfafa faduwar darajar naira da matsalolin canji, sakamakon rashin samun kudade a bankuna da tsarin hada-hadar kudi, babu shakka zai taimaka wajen faduwar darajar naira. Yayin da karancin naira ke yaduwa, bukatar musayar kudaden waje za ta karu a matsayin madadin wanda zai kara dagula darajar naira. Wannan yanayi, yana shafar ikon saye na Dan Adam, yana kuma kara wa rikidar yanayin tattalin arziki da ya riga ya shiga mawuyacin hali.
- B Tabarbarewar kudi daga bankuna, ‘yan kasuwa tare da daidaikun mutane za su iya rike tsabar kudadensu, su ki kai wa bankuna, wanda wannan na iya jawo rashin kudaden a bankuna.
Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsoshi
- Shin za a samu matsala a tsarin biyan dijital? Mai yiwuwa saboda rashin samun kudi, kwatsam ana iya ta’azzara tsarin biyan kudi na dijital kamar yadda aka gani a ‘yan watannin baya, lokacin da aka samu cikas a tsarin sake fasalin naira lokacin Emefiele. Ba duk mutane da kasuwanci ba ne suka canza sheka zuwa mu’amalolin dijital ba.
- Me ya sa babban bankin ya kasa sa-baki? Babban bankin Nijeriya na taka muhimmiyar rawa, wajen tabbatar da daidaiton tsarin hada-hadar kudi. Kodayake, sabbin jagororin babban bankin Nijeriya; da alamu akwai ayoyin tambaya a kwarewarsu wajen gudanar da babban bankin kasa. Ma’ana, ikonsu na gudanar da manufofin kudi yadda ya kamata; yana fuskantar kalubale.
- Akwai hadarin rugujewar bankuna? Mai yiwuwa kasancewar rashin samun kudi na tsawon lokaci; zai kara hadarin lokacin da masu ajiya suka fahimci cewa, ba sa iya samun kudinsu a lokacin da suka bukata, sun rasa kwarin gwiwa da amincewa da tsarin banki, wanda hakan zai haifar da barazana tare da sanya su gaggawar cire kudaden nasu daga bankuna, kamar yadda Lebanon ta samu kanta a ciki.
A karshe, karancin kudin da ake fama da shi yanzu; matsala ce mai yawan gaske tare da rashin fa’ida, wanda yana kuma iya haifar da babbar barazana ga kwanciyar hankali da nagarta a fannin bankuna da kuma tsarin hada-hadar kudi.