Connect with us

LABARAI

Gwamantin Jihar Zamfara Za Ta Kaddamar Da Saida Takin Bana 

Published

on

Kungiyar Manoma ta jihar Zamfara,karkashin jagorancin,shugaba kungiyar na jihar , Alhaji Hafiz Alkali ya tabbatar da cewa, Gwamnatin jihar Zamfara,karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun, ta gama shirinta tsaf dan kaddamar da takin na bana a mako mai zuwa.

Shugaban kungiyar,Hafiz Alkali ya bayyana haka ne a loakcin da ya ke amsa tanbayoyin manaima labarai a ofishinsa da ke Gusau,babban birnin jihar Zamfara.

Hafiz Alkali ya kara da cewa, sakamakon share watannin uku da mu kayi na matsalar annobar Korona ne ya kawo jinkirin kaddamar da saida takin ga manoman jihar Zamfara. amma yanzu cikin kudurar Allah ya sanya gwamnatin jihar Zamfara,karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun ta gama ashirin ta tsafa na fara saida takin a fadin jihar ta Zamfara.

“Kuma wannan karon kungiyoyi manoma zasu jagorancin saida takin da ganin kowane manomi ya samu takin akan lokaci da kuma rangwamen farashi daga gwamnati.

Shugaban ya kara da cewa, Sanyan kungiyoyin manoma cikin jagorancin saida takin da gwamnatin zatayi zai taimaka gaya wajan ganin duk inda manomi ya ke ya samu taki.kuma ba kungiyoyin mu taki rigakafin na ganin ba a karkatar takin ba zuwa wasu jahohin.

Hafiz Alkali ya kuma jinjina wa gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun akan sulhu da Mahara da akeyi a yanzu haka,wannan zaitaimaka wajan ganin wuraren da Noma baisamu ba a bara a wannan shekarar an nomashi.

A kan haka ne muke kira ga alumar jihar Zamfara da su cigaba da yima wannan gwamnatin addu’a karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun dan kudirinsa ya cika na samun dawamamen zaman lafiya a jihar mu ta Zamfara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: