Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Kano ya musanta zargin da tsohon SSG Abdullahi Baffa Bichi ya yi na cewa gwamnatin Kwankwasiyya ta yi almubazzaranci sau fiye 10 da gwamnatin Ganduje ta yi. Ya bayyana haka ne a taron ‘yan majalisa 484, inda ya ce ba za su a yarda da zagi ga shugaban Kwankwasiyya Rabiu Kwankwaso ba.
“Wannan tsohon ma’aikaci ya yi iƙirarin ƙarya cewa Kwankwaso yana karɓar N2 biliyan kowane wata daga asusun jihar,” in ji Gwamna Yusuf. “Me ya sa bai faɗi wannan ba lokacin da yake aiki ba? Muna girmama shugabanni, ba za mu yarda da wulaƙanci ba.”
- Sarki Sanusi II Zai Sake Ayyana Wata Rana Ta Naɗa Sabon Hakimin Bichi
- An Roki Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Tallafi Ga Aikin Hajjin 2025
Gwamnan ya yi kira ga gidajen Rediyo da su daina watsa kalaman ɓatanci,
“Shugabanmu Kwankwaso ya yi aiki a manyan muƙamai – ba za mu yarda a zage shi ba,” in ji Gwamna Yusuf. “Duk inda ya je, za mu bi shi. Ba mu da nadamar wannan zancen.”
Ya kuma bayyana cewa duk wanda ya yi satar kuɗaɗen jama’a ba zai sami wuri a gwamnatin sa ba.
A wani ɓangare na kuma, Gwamna Yusuf ya yi alƙawarin gyara dukkan shalƙwatar ƙananan hukumomi don inganta tattalin arziƙi da tsaro. Ya kuma yi wa ‘yan majalisa alƙawarin tallafawa ayyukan al’umma musamman a fannonin ilimi, lafiya da noma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp