Bayan nasarar da Allah Madaukakin Sarki ya bai wa Gwamnan Jihar Kano Eng Abba Kabir Yusuf a kotun koli ta Nijeriya bisa tabbatar da zaben sa, Jihar Kano na bukatar sabuwar alkiblar jagoranci da ta gaza samu tun dawowar mulkin demokradiyya a shekarar 1999.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar assasawa da gudanar da jagorancin da zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da bunkasar arzikin Jihar Kano ta hanyar dinke baraka ta bangarori da dama, musamman na siyasa, malamai da masarautu, don samun nasarar gudanar da mulkin adalci ga jama’ar Jihar Kano. Mai girma Gwamna ya na da kyakyawan abin koyi daga rayuwar fiyayyen halitta, Annabin mu Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, dangane da kalubalen da ya fuskanta a karon farko, da kuma daga bisani yayin da budi da nasarar Ubangiji Allah su ka saukar masa.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
- Jihar Kaduna Za Ta Ƙarfafa Ƙawancen Tattalin Arziki Da Ƙasar Jamus
A karon farko, yayin halin tsanani da jarrrabawa na tsawon shekaru goma sha uku a garin Makka, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rayu cikin kyawawan dabi’u, kamar dogaro ga Allah, juriya, rashin tsoro, hakuri, da su ka bayyana yayin halin gwagwarmaya wadanda ba za a iya fahimtarsu ba a cikin halin yalwa da iko. Ya kuma ci gaba da isar da sako ba tare da gajiyawa ba duk da rashin yawan mabiya da kuma tsangwama da ya yi ta fuskanta. Wannan juriya da tsaiwa tsayin daka a kan kira ga Allah ya ja hankulan da yawa daga cikin wadanda ba su ba da gaskiya ba suka musulunta. A kashi na biyu na rayuwarsa, wato lokacin da nasara ta samu, iko da mulki suka samu Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya bayyana kyawawan halaye kamar su hangen nesa, yafiya, kauna, saukin kai, da jajircewa, wadanda su ka kara jawo hankulan mutane da dama ya zuwa musulunci. Ya yafe wa wadanda suka nuna masa tsana da kiyayya, ya ba da cikakken tsaro da kariya ga wadanda suka fitar da shi daga mahaifarsa (Makka), ya ba da dukiya mai yawa ga matalautansu. Wadannan kyawawan dabi’u ya sa ko da wadanda ke adawa su ka karbi kiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma duk tsirarun makiyansa suke zama masu kaunarsa daga bisani.
Hakika mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na da kyakyawan darussa daga rayuwar Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata gare shi a halin tsanani da ya shiga tun zaben 2019, sanda bai sami nasarar zama Gwamnan Kano ba, da kuma halin nasarar sa a yanzu da ya yi nasara a zaben 2023 kuma kotun koli ta Nijeriya ta tabbatar masa da wannan Nasara. Gwamna Abba Kabir Yusuf na bukatar dinke baraka a wannan lokaci, ta hanyar yafiya, musamman ga wadanda su ka tsangwame shi a baya da kuma kyakyawan hangen nesa, nuna kauna, saukin kai, da jajircewa, da kare hakkin duk wani mai hakki ba tare da nuna bambanci ta kowannen bangare ba.
Jinjina ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf don kafa Majalisar Dattawan Kano (KEC), wadda za ta zama mai ba da shawara ga gwamnati, kuma ta hada da muhimman jagorori ‘yan asalin Jihar Kano, da kuma tshofaffin gwamnonin ta, Dr Rabiu Musa Kwankwaso, Malam Ibrahim Shekarau da Kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje. Har wa yau, mu na kira da babban murya musamman ga wadannan shuwagabanni uku da su ka mulki jama’ar Kano tun daga 1999 zuwa yanzu, su kau da banbance-banbancen da ke tsakanin su wajen tallafa wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf don samar wa Jihar Kano sabuwar alkiblar shugabanci na gari. Hakika a tsawon shekaru kusan 24, kowanne daga cikikin wadannan shuwagabanni ya ba da gudunmawa, gwargwadon ikon su, wajen samar da ayyukan ci gaba ta bangarori da dama a Jihar Kano. A yanzu ne mutanen Kano su ka fi bukatara gudunmawarku wajen wanzar da abubuwan alkhairai da ku ka dasa, da kuma cike gurabun da ku ka bari, don bunkasar Jihar Kano a Nijeriya da duniya gaba daya. Hakika za su zamanto ababen alfahari a gare mu in har wannan tsari ya tabbata.
Shi fa kyakyawan shugabanci mai dorewa, ya na samuwa ne lokacin da aka samu jagororin da su ka cancanta daga cikin al’uma, kuma ma su zartar da kudurorin da su ka dace a lokutan da su ka dace, domin tunkara da warware matsalolin da ke addabar al’umar su a wannan lokaci. Lallai Kanawa na matukar kishirwar ingantaccen shugabanci tare da hadin guiwar dukkanin masu ruwa da tsaki daga shuwagabannin siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa, ma’aikata, ma su manya da kananan sana’o’i da matasa da dukkanin jama’a. Don haka dole ne a rage, ko a kawar da banbance-banbancen siyasa da kiyayya a tsakanin shuwagabanni da mabiya a wannan jiha tamu, domin mu tunkari manyan matsalolin mu na cin hanci da rashawa, magudin zabe, matsanancin talauci, tabarbarewar ilimi, lafiya da tattalin arziki da kuma siyasar rashin kishin talaka ta hanyar yawan ketarawar daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar don maslahar kawunan su.
Kano na bukatar sabuwar alkibla don wanzar da matsayin ta na cibiyar kasuwanci da al’adu da siyasar Arewacin Nijeriya. Allah Madaukakin Sarki ya shiryar da shuwagabannin mu, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya da yalwar arziki mai amfani, amin.