Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya gabatar da kudi naira biliyan 178,576,000,000 a gaban majalisar dokokin jihar a matsayin kudirin kasafin kudi na shekarar 2023.
A cewar Gwamnan, “An ware Naira Biliyan 56.54 kudin Ma’aikata, Naira biliyan 89.4 an ware su ne domin zuba jari wanda kuma shine wanda ya lashe kusan rabin kasafin kudin da aka tsara”.
“Haka kuma, an ware kimanin Naira biliyan 25.43 domin kula da ayyukan yau da kullum na ma’aikatu, da hukumomi da sauran abubuwa masu bijurowa na yau da kullun”.
Gwamna Badaru ya bayyana cewa kasafin kudin da aka yi wa fannin ilimi da lafiya ya kai kimanin Naira biliyan 61.2 da kuma Naira biliyan 28.9.
Sai dai Gwamnan ya yabawa Majalisar Dokokin Jihar bisa kokarin da suka yi na samun nasarar aiwatar da kusan kashi 80% na kasafin kudin 2022.
Sai dai ya bukaci majalisar da ta yi gaggawar amincewa da kudurin kasafin kudin ayyukkan jihar.
Kakakin majalisar dokokin jihar Rt. Idris Garba Jahun ya bada tabbacin yin bincike cikin gaggawa tare da zartar da kasafin kudin kafin karshen watan Disamba na 2022.