Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya kaddamar da rabon sama da Naira miliyan 500 ga mutane sama da 4,000 da za su ci gajiyar shirin nan na KB CARES a jihar.
A karkashin shirin na hadin guiwa tsakanin gwamnatin Jihar Kebbi da Gwamnatin Tarayya a karkashin Muhammadu Buhari, ‘yan kasuwa 1,950 ne za su ci gajiyar shirin da za su samu Naira dubu 20,000 a wata biyu har na tsawon watanni 24.
- Lauyoyin Arewa Sun Zargi EFCC Da Nuna Wariya Kan Wadanda Ake Zargi Da Badakalar Kudade
- Peng Liyuan Ta Ziyarci Dakin Adana Kayan Tarihi Na Fasaha Na Birnin Ayutthaya Na Thailand
Da yake jawabi a wajen taron, Bagudu ya kuma yi magana kan shirin NG-CARES da cewa wani shiri ne na shiga tsakanin Bankin Duniya, Gwamnatin Tarayya da kuma gwamnatocin Jihohi ga al’umma da kuma ‘yan kasuwa a duk fadin Kasar nan.
A cewar Bagudu, shirin an yi shi ne don rage tasirin cutar Korona ta hanyar zaman gida da ya biyo bayan barkewar cutar a duniya ciki har da Nijeriya.
Gwamnan, ya ce zaman gidan ya sanya mutanen duniya sun kasance a gida ba tare da samun damar yin duk wani aiki mai ma’ana na zamantakewa da gudanar da ayyukansu ta hanyar rashin habaka tattalin arziki.
Haka zalika, ya kara da cewa, “An raba shirin zuwa sassa da dama inda manoma da dama suka samu takin zamani da kayan masarufi da sinadarai da sauran kayayyakin aiki gona a kyauta.”
Gwamnan dai ya kuma ce taron na musamman ne domin kaddamar da wasu manyan tallafi guda biyu ga al’ummar jihar.
Har-ila-yau Gwamna ya ce, “A karkashin tsarin musayar al’umma, kasa da 1,9500 ne za a bai wa daga N100,000 zuwa N120,000, sau daya. Haka kuma kudaden na wannan fanni sun riga sun kasance a bankunan kasuwanci a fadin jiha kuma an fara raba kudaden.”
Shi ma da yake nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Dakta Abba Sani Kalgo ya yaba wa kokarin Gwamna Bagudu na ganin an samu nasarar aiwatar da shirin.
Ya kuma bayyana cewa gwamnan ya ci gaba da jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.
A cewarsa, “Bayan kaddamar da shirin za a raba sama da naira miliyan 400 zuwa ga mutane 1,950 yayin da wasu kananan ayyuka aka gudanar a kananan hukumomi 13.”