Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Hakimin Pali kuma Yariman Bauchi, Alhaji Garba Muhammad Sambo. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi bisa wannan rashin.
Yariman Bauchi ya rasu ne a ranar Talata a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, bayan gajeruwar rashin lafiya.
- An Kama Mata Da Mahaifiyar Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Ado Aliero A Saudiyya
- Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
A saƙon jaje da ya fitar ta hannun kakakinsa Mukhtar Gidado, gwamna Bala Muhammad ya nuna kaɗuwa sosai da rasuwar basaraken da ya kasance dattijo mai dattako.
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.
Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.
“Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.
Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin..
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp