Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da lambar yabo ta Nigeria Excellence in Public Service (NEAPS) ta 2025 saboda gudummawar da ya bayar wajen inganta mulki da tsaro a jihar. An gabatar da kyautar ne a wani taron liyafar cin abinci a Aso Rock, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilci shugaban ƙasa. A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, taron ya samu shiriyawar The Best Strategic Media (TBS) da haɗin gwuiwar SGF.
An bayyana cewa Gwamna Lawal ya samu wannan yabo ne saboda manyan gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da ya shafe a ofis. Daga cikin muhimman abubuwan da ya cimma akwai biyan sama da naira biliyan 15 da aka rike wa ma’aikatan Zamfara na tsawon shekaru 13, da kuma daga mafi karancin albashi daga N7,000 zuwa N70,000. Gwamnatin ta kuma tabbatar da biyan albashin watanni 13 da wasu karin tallafi ga ma’aikata.
- Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10
- Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Na 2026 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
A fannin more rayuwa da ilimi, an bayyana yadda gwamnan ya jagoranci sabunta birane, tare da sake ginawa da gyara makarantun gwamnati sama da 500 a faɗin jihar. Haka zalika, an samu ci gaba a fannin lafiya ta hanyar gyaran asibitoci da samar da kayan aiki ga cibiyoyin kiwon lafiya domin inganta ayyuka ga al’umma.
A ɓangaren tsaro, NEAPS ta jaddada nasarorin Gwamna Lawal da suka haɗa da kafa Jami’an Kare Al’umma, samar da motocin aiki da mai ga rundunonin Soji, da sayo kayan aikin tsaro, da bayar da tallafi akai-akai ga jami’an tsaro. Wannan karramawa, a cewar sanarwar, za ta ƙara ƙarfafa masa gwuiwar ci gaba da aikin farfaɗowa da sake gina jihar Zamfara.














