Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, lamarin da ya kawo ƙarshen raɗe-raɗi game da makomarsa a siyasa.
Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah ne, ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
- 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
- Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima
Sai dai, gwamnan bai fice daga jam’iyyar shi kaɗai ba, domin mambobi 23 na Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, sun sanar da ficewarsu daga PDP tare da bin sahunsa.
Alabrah ya rubuta cewa:, “Gwamna Douye Diri ya fice daga PDP tare da mambobi 23 na Majalisar Dokokin Jihar.”
Wannan sauyin siyasa na cikin manyan abubuwan da suka taɓa faruwa a tarihin siyasar jihar, kuma ya haifar da shakku kan makomar jam’iyyar PDP, wadda ta daɗe tana mulkin jihar tun daga 1999.
Ko da yake ba a bayyana dalilin ficewarsu ba, masu sharhi kan harkokin siyasa suna ganin hakan na da nasaba da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar ke fama da shi, sannan ana zaton Gwamna Diri zai koma APC.
Mutane da dama a faɗin jihar sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin yayin da ake jiran mataki na gaba da gwamnan zai ɗauka.