A ranar Larabar nan da ta gabata Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya tsallaka rijiya da baya bayan motarsa ta kama da wuta a Jihar Legas.
Al’amarin ya faru ne a hanyar filin jirgin sama da ke Ikeja. Mai taimaka wa Gwamnan a kan sadarwa, Lere Olayinka ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Y ace al’amarin ya faru ne a yayin da Gwamnan yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama, sannan ya ƙara da cewa, “lallai da farko an tsara cewa zai shiga wannan motar da ta ƙone ne amma kuma sai ya zamo bai shiga ba, Allah ya kiyaye”.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton dai babu cikakken labarin abin da ya haddasa ƙonewar motar, sannan Gwamnan ya ƙi cewa uffan game da abin da ya faru.
Motar dai ta ƙone ƙurmus!