Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, CON, ya amince da naɗin sabbin sarakuna a sabbin masarautu guda bakwai da aka ƙirƙiro a jihar.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaran gwamna, Humwashi Wonosikou, an bayyana sabbin sarakunan da aka naɗa a matsayin:
- Wang Yi Zai Kai Ziyara Kasashen Namibia, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Chadi Da Najeriya
- Harry Maguire Ya Sanya Hannun Kwantaragin Shekara Ɗaya A Manchester United
- HRH Alhaji Sani Ahmadu Ribadu: Sarkin Fufore
- HRH Barrister Alheri B. Nyako: Tol Huba
- HRH Farfesa Bulus Luka Gadiga: Mbege Ka Michika
- HRH Dr Ali Danburam (MBBS, FWACP, FCCP): Ptil Madagali
- HRH Aggrey Ali: Kumu of Gombi
- HRH Ahmadu Saibaru: Sarkin Maiha
- HRH John Dio: Gubo Yungur
Gwamna Fintiri ya taya sabbin sarakunan murna, inda ya jaddada cewa zaɓen da aka yi an yi shi ne bisa cancanta da farin jinin su a cikin al’umma.
Ya buƙace su da su kasance masu gaskiya da riƙon amana a yayin gudanar da ayyuka da shugabancinsu.