Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa game da rasuwar fitaccen dan jarida Malam Shehu Saulawa na Gidan Rediyon Faransa RFI, wanda ya rasu a ranar Litinin a Bauchi bayan ya yi fama da jinya mai tsawo.
A sakon sa na ta’aziyya dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe, Gwamna Inuwa ya bayyana marigayin dan jaridan na kasa da kasa a matsayin kwararre a harkar yada labarai wanda ya nuna kwarewa da sanin makama yayin da yake aiki a kafofin yada labarai daban-daban, ciki har da gidan rediyon BBC.
- Gobara Ta Yi Sanadin Asarar Dukiya Mai Yawa A Jere
- An Kama Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai A Kano
Ya ce mutuwar Saulawa za ta haifar da babban gibi a fagen aikin jarida, ba wai a arewacin Nijeriya kadai ba, har ma da qasa baki daya.
A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, Gwamna Inuwa, ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin, da abokan aikin sa da kuma mahukunta da ma’aikatan gidan rediyon RFI bisa wannan babban rashi da aka yi, yana mai addu’ar Allah ya jikan sa da rahama ya sa Aljannah Firdausi ce makomarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp