Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya fara raba tallafin kuɗi ga ɗalibai ‘yan mata 8,225 da ke cikin ƙananan hukumomi 14 na jihar.
An fara rabon ne a ranar Laraba a ɗakin taro na Garba Nadama da ke sakatariyar JB Yakubu a Gusau, ƙarƙashin shirye-shiryen ACReSAL da AGILE.
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Yaƙi Da Masu Damfara A Intanet
- Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Kafa Makomar Halittun Duniya Ta Bai Daya
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, an zaɓi waɗannan daliban ne duba da yanayin iyayensu masu ƙaramin ƙarfi domin a taimaka musu su ci gaba da karatu.
Kowace ɗaliba za ta karɓi Naira 40,000 a zangon farko, sannan a zangon karatu na biyu da na uku, za a ƙara mata Naira 10,000, hakan na nufin kowace za ta samu Naira 60,000 a shekara.
An riga an ware Naira miliyan 132 domin rukuni na farko, kuma an fara shirin rukuni na biyu.
A wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ƙarƙashin shirin ACReSAL, an raba tallafi ga mutum 500 a Gusau, Bungudu da Ƙaura Namoda, domin inganta harkar noma da farfaɗo da tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa, “Wannan tallafin zai ci gaba da yawo a faɗin jihar, kuma mutane da dama za su ci gajiyarsa. Idan aka yi amfani da damar yadda ya kamata, to za a samu ci gaba sosai.”
Gwamnan ya bayyana cewa ilimi na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kai, musamman na ‘yan mata.
Ya ce, “Mun ɗauki matakai na kawar da duk wani cikas da zai hana ‘yan mata su kammala karatunsu. Idan ka ilmantar da yarinya, ka ilmantar da al’umma gaba ɗaya.”
Ya yaba wa ma’aikatar muhalli da ta ilimi saboda jajircewarsu wajen ganin shirin ya yi nasara.
A ƙarshe, ya roƙi waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata domin amfanin kansu da iyalansu da kuma al’umma baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp