Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya gabatar da kasafin kudi naira biliyan 250, 134, 091, 757.01 na shekarar 2024 na samar da ababen more rayuwa da kuma ayyukkan ciyar da al’ummar jihar a gaban majalisar dokoki don damar amincewa da kasafin kudin.
Dakta Nasir ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a zauren majalisar da ke Birnin Kebbi.
- Bunkasuwar Sin Na Taka Rawa Ga Farfadowar Yankin Asiya Da Pacific
- BRICS Ta Bi Sahun Sassan Dake Neman Kawo Karshen Rikicin Isra’ila Da Palasdinu
Kasafin kudin samar da ababen more rayuwa da karfafa wa al’ummar jihar da kuma biyan bukatun ‘yan jihar da kuma cika alkawuran da aka dauka a yayin yakin neman zabe da aka yi wa jama’armu.
Gwamnan, ya ce a yayin gabatar da kasafin kudin na shekarar 2024 da za a kashe kudaden da ake kashewa akai-akai na biliyan 90.6, yayin da manyan kudaden da za a kashe ya kai biliyan 159.4.
Wasu muhimman sassa na tattalin arzikin jihar sun samu karin kasafin kudi saboda matakin da gwamnati ta dauka na samar da sabon shirin jihar Kebbi.
Ya ce wani bangare na shirin shi ne “magance batutuwan da suka hada da samar da ayyukan yi ga matasa da mata, gyara makarantu, gina hanyoyi, tsaro da samar da ingantaccen ruwan sha da kalubalen muhalli a jihar.
“A karkashin kasafin kudin 2024, nan take za mu kara habaka manufofinmu da aka tsara da kuma dorewar shirinmu a jihar”.
Dokta Nasir ya ce shirin gwamnatin na samar da ababen more rayuwa zai yi nisa wajen samar da hanyoyin samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar al’ummar jihar ta Kebbi kai tsaye, wanda hakan zai shafi al’ummar Jihar Kebbi kai tsaye, inda ya kara da cewa irin wannan shirin zai shafi gyaran makarantu da gina tituna da kuma zamanantar da jihar.
“Kudirin kasafin kudin shekarar 2024 na nuni da cewa an zuba jari mai yawa wajen samar da ingantaccen ruwan sha, da karfafawa mata da kungiyoyin matasa ta hanyar samar da ayyukkan yi.
Ya kuma ba da tabbacin ga ‘yan majalisar jihar na ci gaba da zaman lafiya da zamantakewar aiki.
Yayin da yake jinjina wa majalisar dokokin jihar kan kokarin da suke yi na nuna kyakykyawan sakamako doka ga daukacin al’ummar jihar.
A nasa martanin, kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Usman Muhammad ya bai wa gwamna Nasir Idris tabbacin yin gaggawar amincewa da kasafin kudin shekarar 2024 da aka gabatar wa majalisar domin amincewa.
Yayin da yake yi wa gwamnan alkawarin tabbataci da kasafin kudin da za a kashe zai biya bukatun ‘yan jihar domin ‘yan majalisar su ma wakilan jama’ar jihar ne daga mazabu daban-daban na jihar.
Daga karshe ya gode wa gwamna Nasir Idris bisa jajircewarsa ga ci gaban jihar da al’ummarta.