Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya ziyarci Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar IPOB a gidan yari da ke Jihar Sakkwato.
Daga cikin waɗanda suka raka shi akwai, ɗan uwansa Emmanuel Kanu, Lauyan Jihar Abia Ikechukwu Uwanna, da mai ba shi shawara kan harkokin kafofin watsa labarai, Ferdinand Ekeoma.
- Gwamna Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
- Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Haƙar Ma’adinai Na Tsawon Watanni 6
Gwamna Otti ya shawarci Kanu da ya zama mai nutssuwa da ƙarfin hali, yana mai tabbatar masa cewa yana ƙoƙari don gani a na sake shi.
Haka kuma ya ce Sarkin Musulmi yana goyon bayan sakin Kanu kuma yana son a rage tashin hankali.
Ziyarar na zuwa ne makonni biyu bayan hukuncin ɗaurin rai da rai a kotun tarayya a Abuja, ta yi wa Kani bisa laifin ta’addanci.
Kotun ta kuma haramta masa amfani da wayoyi da kafofin sada zumunta sai a ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro.














