Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin kammalawa tare da kaddamar da wani asibitin kwararru mai gadaje 300 wanda aka tanada musamman don kula da masu cutar kansa a Millennium city, da ke Kaduna a karshen shekarar 2024.
Wannan aikin asibitin wanda tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya kaddamar, ya samu tallafin dala miliyan 148 daga bankin cigaban Musulunci (IDB) da nufin samar da cikakkiyar cibiyar kiwon lafiya ga al’ummar jihar Kaduna.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC
- Sanatocin Arewa 12 Da Suka Gaza Gabatar Da Ƙudiri A Watanni 15
Duk da kokarin da gwamnatocin baya da suka hada da na Patrick Yakowa, Mukhtar Ramadan Yero, da Nasir Ahmed El-Rufai suka yi, har yanzu aikin bai kammala ba.
Da take magana, kwamishiniyar lafiya ta jihar Hajia Umma K. Ahmed a wani taron manema labarai a ranar Laraba, da take bayyana irin nasarorin da gwamnatin Sanata uba Sani ta samu a fannin kiwon lafiya, ta ce, Gwamna Sani ya ce: “A cikin zango na karshe na shekarar 2024, zai gayyace ‘yan jarida domin kaddamar da kammala ginin wannan katafariyar cibiyar kiwon lafiya ta zamani.
“Kaddamar da wannan cibiya ta zamani, za ta kawo sauyi tare da gyara harkokin kiwon lafiya na Jiha tare da rage yawan fita zuwa kasashen ketare don neman magani, domin asibitin mai gadaje 300 yana da sashen binciken cututtukan daji da kuma magance cutar. ”
Gwamnan ya ce, tsaren-tsaren inganta kiwon lafiya ya bada fifiko matuka wajen samar da kayan aiki a dukkan matakan kiwon lafiya da suka hada da na farko, matsakaita da manya a jihar, inda ya ce, gwamnati na inganta manyan asibitoci 9, inda aka zabo uku-uku daga cikin shiyyoyi Uku da ke jihar.
“Asibitocin sun hada da Asibitin Maigana, Asibitin Rigasa, Asibitin Gwantu, Asibitin Ikara, Asibitin Patrick Ibrahim Yakowa, da Asibitin Giwa.”
Sauran sun hada da “Sabon Asibitin Tunawa da Dabo Lere, Asibitin Sabon Tasha, da Asibitin Kachia”. in ji ta.
Wadannan Asibitocin, a halin yanzu suna cikin matakai daban-daban na sake ginawa, sake fasali, da kuma samar da kayan aiki a matsayin wani bangare na shirin Gwamnati na inganta cibiyoyin kiwon lafiya.
Gwamnan ya kara da cewa, ana kokarin samar da ababen more rayuwa ne domin ganin an samu sauyi a kowane mataki domin samar da ingantacciyar kulawa ga al’ummar jihar Kaduna.
Hajiya Umma ta jaddada cewa: “Tun da ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Gwamna Uba Sani ya nuna jajircewarsa na kawo sauyi a fannin kiwon lafiya.”