Muhammad Maitela" />

Gwamna Shettima Ya Yaba Da Cikakken Goyon Bayan Da Jama’ar Borno Suka Bashi

Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya bayyana matukar farin ciki tare da nuna matukar godiyar sa ga jama’ar jihar, dangane da halin kauna da cikakken goyon bayan da suka nuna mishi tare da jam’iyyar APC, a zaben ranar Asabar wanda ya gudana- ta hanyar fitowa kwan su da kwarkwata domin ganin jam’iyyar ta kai gaci.
Gwamna Kashim ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo, wanda Malam Isa Gusau; mai taimaka wa Gwamnan a fannin yada labarai, ya aike wa Leadership A Yau. Bidiyon mai dauke da sakon godiyar Gwamnan zuwa ga baki dayan al’ummar jihar, wadanda suka zabi yan takarar jam’iyyar APC a jihar Borno.
Kashim Shettima ya sha alwashin cewa shi da sauran sanatacin jihar; Sanata Mohammed Ali Ndume da Sanata Abubakar Kyari hadi da yan majalisar wakilan jihar 10, zasu tabbatar wajen ganin cewa sun kare muradu tare da bukatun daukwacin jama’ar jihar Borno a zaurukan majalisun tarayya; zubi na tara mai zuwa (9th).
A hannu guda kuma, Gwamna Shettima ya taya sauran takwarorin sa; a karkashin jam’iyya APC, murnar samun nasarar lashe zabukan da ya gudana tare da ankarar da su kan cewa, suna da sauran jan aiki a gaban su, wajen hada hannu wuri guda wajen ganin sun kara samun nasarar cin zaben kujerar gwamna da yan majalisar dokokin jihar, wanda zai gudana ranar 9 ga watan Maris 2019.
Wanda ya bayyana cewa, duk da sanin kowa ne kan cewa jam’iyyar APC a jihar Borno tana da babban sanannen gwarzon mutum- Farfesa Babagana Umara Zulum, son kowa; kin wanda ya rasa, amma dai akwai bukatar ayi kyakkyawan shirin tunkarar zaben da muhimmanci.
Yayin da ya bayyana cewa, “duk da yadda na sani kan cewa ko shakka babu ita kan ta jam’iyyar APC, Farfesa Zulum, tare da yan majalisun dokokin jihar Borno 28, sun yi kyakkyawan shirin samun gagarumar nasara. Duk da wannan, ina sake jadadda kira ga jama’ar jihar Borno su kula da kuri’un su da kyau tare da yin tururuwa domin zabar gwamna tare da yan majalisun dokomlkin jihar, a karkashin jam’iyyar APC”.

Exit mobile version