Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sake ƙaryata zargin cewa yana bai wa masu aikata laifuka mafaka, musamman waɗanda ke haddasa tarzoma a yankunan iyaka tsakanin jihar da Benue.
Wannan bayani ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda tsohon Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Jihar Binuwe, Farfesa Zachary Anger Gundu, ya danganta gwamnan da kashe-kashe a Benue da kuma wawure filaye a Nasarawa.
- Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
- Sarkin Musulmi Ya Nuna Baƙin Ciki Kan Kisan Kiyashi A Binuwe
Da yake ƙarin bayani ga manema labarai a madadin gwamnan, Jami’in hulɗa da jama’a na Gwamna Sule, Ibrahim Addra, ya bayyana takaicinsa kan yadda Farfesa Gundu ya fito fili yana zargin gwamnati ba tare da wata hujja ba a kan irin wannan batu mai sarƙaƙiya kamar matsalar tsaro a iyakar jihohin.
Addra ya bayyana kalaman Farfesa Gundu a matsayin masu tayar da hankali da kuma yin gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin. Ya ce irin wannan zargi ba shi da amfani face tada hankali da kawo Tsaikon ga buƙatar shawo kan matsalar tsaro.
Ya ce Gwamna Sule yana cikin bakin ciki da halin da ake ciki a Binuwe, kuma yana ci gaba da nuna damuwa da alhini a kan kashe-kashen da ke faruwa. Ya kuma gargadi Farfesa Gundu da ya kawo hujjoji na inda ake ajiye ƴan ta’addan da kuma yadda ake raba filaye ga makiyaya a Nasarawa, ko kuma ya fuskanci shari’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp