Gwamna Uba Sani da shugabar kungiyar kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo Iweala, sun kaddamar da ginin katafaren kamfanin hada magunguna (AMA Medical Manufacturing Plant, Limited) ranar Alhamis, a Kudenda da ke, Kaduna.
Dakta Ngozi ta bayyana cewa, kamfanin an samar da shi ne don kasuwanci da zai habaka jihar Kaduna, Nijeriya da ma Nahiyar Afirka baki daya.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 61 A Wani Sabon Hari A Kaduna
- Tallafin Da Amurka Ta Baiwa Gaza Wasan Kwaikwayo Ne
Tun da farko, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a yayin da ya ziyarci kamfanin AMA-MED, ya bayyana cewa, zuba jari a jihar abin a yaba ne kwarai da gaske kuma hakan zai taimaka matuka wajen yaba kokarin gwamnatin jihar Kaduna na bunkasa harkar lafiya.
Gwamnan ya kara da cewa, kamfamin zai taimaka matuka wajen samar da damammaki masu yawa ga al’ummar jihar na daga samar da ayyukan yi, habaka harkar kiwon lafiya da dai sauransu.
Uba Sani ya nuna cewa, jihar Kaduna ce ta daya kan saukin gudanar da kasuwanci a fadin Nijeriya.
“Muna da tsarin kasuwanci mafi inganci a jihar Kaduna, don haka mutane da dama suke zuwa don zuba hannun jarinsu a jihar, kuma ba ni da shakka a raina tare da haɗin gwiwarmu da AMA-MED, za mu sake jawo hankalin wasu masu zuba jari da yawa zuwa jihar.
“Muna da su daga Dubai, Indiya, Indonesia, Morocco wadanda suke tare da mu a jihar kuma a shirye muke mu yi aiki tare da AMA-MED, ba ni da wata shakka a raina, AMA-MED za su zama mafi kyawu kuma babban kamfani a fannin masana’antar kiwon lafiya a duk fadin Nijeriya.
Bikin ya samu halartar wakilan gwamnati, sarakunan gargajiya, manyan ‘yan kasuwa, fitattun masana daga cikin gida da kasashen waje da daidai sauransu.
Daga cikinsu akwai, Wakiliyar Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima; Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; mataimakiyar gwamna, Dr Hadiza; Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate CON; Shugabar Kungiyar kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo Iweala; Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bamalli tare da wasu jami’an gwamnati.