Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya karyata rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa ya bayar da umarnin cire tutocin jam’iyyar PDP daga gidan gwamnati da ke Fatakwal.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da sakataren yada labaran jam’iyyar adawa ta APC a jihar, Senibo Chris Finebone, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar zuwa PDP.
- Zaben Fidda Gwanin PDP: Wike Ya Gurfanar Da Atiku, Tambuwal Da INEC A Gaban Kotu
- Me Ya Sa Ake Rubibin Wike A Siyasar Nijeriya?
A safiyar ranar Juma’a an wayi bari ko’ina a kafafen sada zumunta da hoton Finebone tare da gwamnan jihar Ribas, Wike, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Siminalaye Fubara, da kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, Cif Davies Ibiamu Ikanya, a wata ziyara da suka kai gidan gwamnan a Fatakwal a daren Alhamis.
Wike, wanda ya yi magana a daren Alhamis a Fatakwal, babban birnin jihar, yayin da yake karbar Finebone da Ikanya, ya ce: “Kuna iya tunani kan irin labaran karya da mutane ke yadawa. Ba na bata lokacina akan irin wannan karyar.”
Da yake mayar da martani kan kalaman tsohon kakakin jam’iyyar APC, gwamnan ya yi alkawarin bayar da kwangilar gina titin Opobo Ring kafin ya bar mulki a shekarar 2023.
Ya ce: “Zan bayar da kwangilar titin Opobo Ring Road kuma na kuma tabbatar da cewa an samar da kudin da zan biya kafin in bar ofis a watan Mayun 2023.
“Allah ne yasa danka ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyarmu. Haka Allah zai sa shi ya ci nasara. Ban shirya ba amma Allah ne ya yi. Jama’ar Opobo su rika godewa Allah da jinkansa”.
Da yake tabbatar da komawarsa jam’iyyar PDP mai mulki, Finebone ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa; “Sim Fubara yayana ne.”