Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi kira ga sojojin Nijeriya da ke aiki wajen tabbatar da tsaro a Jihar Katsina sun dunga amsa kiran gaggawa a dukkan yankunan da suke aiki. Ya ce wannan zai ceto al’umma a lokutan hare-haren ‘yan ta’adda.
Gwamna Radda ya yi wannan kira ne lokacin da ya karbi bakuncin Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Taofeek Lagbaja, a yayin wata ziyarar ban girma.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Manoma 6 Da Aka Sace A Katsina
- Babban Taron Samar Da Kayayyaki Na 2024 Ya Sa Kaimi Ga Kulla Ayyukan Hadin Gwiwa 718
Ya ce ya lura da cewa zuwan babban hafsan sojojin Nijeriya da babban hafsan tsaro zuwa Jihar Katsina a cikin mako guda ya tabbatar da damuwar gwamnatin tarayya kan matsalar tsaro da ta addabi jihar. Ya yaba wa kokarin da sojojin Nijeriya suke yi wajen shawo kan kalubalen tsaro a jihar.
A cewarsa, hadin gwiwar jami’an tsaro ya sa aka samu kwanciyar hankali wanda ya bai wa manoma damar yin noma a daminan bana a jihar. Sai dai, ya yi kira da a kara daukar matakai don tabbatar da ganin manoma sun kwashe amfanin gonakinsu cikin aminci.
Gwamna Radda wanda ya nuna damuwarsa game da yadda al’umma ba sa iya tinkarar ‘yan ta’adda. Ya ce tuni gwamnatin jihar ta fara wayar da kan jama’a kan hakan kuma ta umurci malamai su yi kira kan muhimmancin kare kai.
Tun da farko, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftananar Janar Teofeek Lagbaja, ya ce ya zo Katsina ne a wani bangare na ziyarar da yake yi wa sansanonin soja domin duba ayyukansu da kuma yanayin huldarsu da fararen hula. Yana mai cewa idan aka hada kai za a iya shawo kan kalubalen tsaro.