Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya mika motocin bas guda 10 na CNG ga kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar.
Motocin bas din da gwamnatin tarayya ta bayar na daga cikin matakan rage radadin cire tallafin man fetur ga ma’aikata.
- Tattalin Arziki: Gwamna Lawal Ya Nemi Hadin Gwiwar Masu Zuba Jari Na Kasashen Afirka A Taron AFREXIM A Kenya
- Rundunar Sojin Haɗin Gwiwa Ta Ƙasashe Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 15 A Borno
Gwamna Yusuf ya mika bas din ga shugaban kungiyar NLC, Mista Joe Ajaero a wajen bikin da aka gudanar a sakatariyar kungiyar ta NLC da ke Kano.
A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya yabawa gwamnatin tarayya bisa jajircewar da ta yi na sassauta kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta tare da yaba wa kungiyar NLC bisa yadda take fafutukar ganin an kyautata rayuwar ma’aikata.
Ya yi kira ga ma’aikata a jihar da su mayar da alkairi ta hanyar sadaukarwa, wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen cimma muradun ci gaban jihar.
Shugaban NLC ya bayyana tallafin a matsayin wani gagarumin mataki na inganta rayuwar ma’aikata.
Ajaero ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na tallafawa ma’aikata da suka hada da gaggauta biyan albashi da kuma aiwatar da mafi karancin albashi.