A kokarin sa wajen yaki da talauci da zaman kashe wando, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bai wa masu kanana da matsakaitan sana’o’in hannu kimanin 704 tallafin naira miliyan 32 a jihar, wanda idan an hada wannan adadin da wanda ya raba a makon da ya gabata a jimlace sun kama naira miliyan 154 ga kananan yan kasuwar, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya kaddamar da bayar da tallafin ga kananan yan kasuwa kimanin 304 da ke kan hanyar Damboa, wanda kowane ya samu tallafin 50,000, kana da mutum 400 a unguwar Kulo Gumna wadanda kowane ya ci gajiyar tallafin 50,000, duka a birnin Maiduguri.
A hannu guda, kimanin naira miliyan 35.2 aka raba wa masu kananan masana’antu a ranar Lahadin, wanda kafin hakan masu sana’ar sayar da goro ma sun samu tallafin gwamnatin jihar na naira miliyan 75 don karfafa sana’ar su, sannan da karin wasu naira miliyan 20 wadanda aka bayar da su tallafi ga masu shagunan kan titi Dandal a birnin tare da karin naira miliyan 24 ga yan kasuwar da ke zaune a unguwar Shatale-taken Custom duka a Maiduguri- yayin da kowane dan kasuwa ya samu tallafin 50,000.
Da ya ke jawabi ga wadanda su ka ci gajiyar tallafin, Gwamna Zulum ya bukaci kananan yan kasuwar su yi amfani da tallafin ta hanyar da ya kamata tare da tunatar musu cewa wannan tallafin ya na daya daga cikin alkawuran da ya dauka wa al’ummar jihar a lokacin yakin neman zabe.
”Bugu da kari, tallafa wa jama’a ya na daga cikin jerin manufofinmu 10 wadanda mu ka dauki alkawarin aiwatar dasu a lokacin yakin neman zabe, inda mu ka ce za mu tallafa wa jama’ar mu domin dogaro da kansu. Kana kuma ina rokon wadanda su ka ci gajiyar wannan tallafin su gudanar dashi bisa ka’ida tare da ririta shi don ya amfanar.”
A gefe guda, kafin Zulum ya kaddamar da bayar da tallafin, Babban Manajan bankin ‘Microfinance’ a jihar Borno, Dr. Bello A. Ibrahim ya bayyana cewa kawowa yanzu, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi ga kungiyoyin yan kasuwa daban-daban sama da naira biliyan daya (N1 billion).
Ya ce a Disamban 2019, Zulum ya tallafa wa mabarata naira miliyan 384, yayin da kuma a cikin Janairun 2020, gwamnatin jihar ta ware naira miliyan 515 ga yan bangar siyasar nan ta ‘Ecomog’ su kimanin 2,862 a kokarin jihar Borno na dakile hadurran bangar siyasa- wanda aka rinka basu naira 30,000 tsawon wata shida.