Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya amince da murabus kashin kai da Babban Sakataren Lamuran Sirrinsa (PPS), Dakta Muhammad Musa Kirfi ya yi. Idan za ku iya tunawa dai, mun kawo muku labarin da ke cewa PPS din gwamnan ya yi murabus daga mukaminsa, duk kuwa da cewa babu wani cikakken bayanin dalilin ajiye aikin nasa, sai dai Gwamnatin jihar ta ce ya ajiye aikin ne bisa ra’ayin kansa kuma sun amshi hakan hannu biyu-biyu.
Gwamnan ta cikin sanarwar manema labarai da Kakakinsa Muktar Gidado ya sanya wa hannu gami da fitarwa a daren nan, ya lura kan cewa ajiye aikin na Kirfi ya fara aiki ne tun daga ranar 21 ga Janairun 2021.
Sanarwar ta Gidado na cewa: “Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya amince da ajiye aiki bisa radin kashin kai da Principal Private Secretary (PPS), Dakta Mohammed Musa Kirfi ya yi wanda ya fara aiki daga ranar 21 ga watan Janairun 2021.