Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir ya gabatar da naira biliyan N202, 641, 558, 614 .46 a matsayin kasafin kudin shekara 2023 da suka kunshi sashin manyan ayyuka da kuma ayyukan yau da kullum.
A kasafin, Gwamnatin ta ware naira biliyan N87, 923, 242, 953. 50 kwatankwacin kaso 43 a matsayin kudaden gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma naira biyar N114, 714, 515, 650. 97 kwatankwacin kaso 57 cikin dari na kasafin a matsayin na gudanar da manyan ayyuka.
Da ya ke gabatar da kasafin kudin adi a kwaryar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya bayyana cewar kasadin 2023 ya samu kari da kaso 2.6 na kasafin 2022 na naira biliyan N195, 355,607, 143.
Ya ce, karin kasafin ya biyo bayan halin da ake ciki na tattalin arziki a kasar nan kuma an yi zurfin tunani wajen ganin an tabbatar da cewa an gudanar da ayyukan da aka tsara gudanar da su yadda ya kamata.
Bala ya kara da cewa kafin kammala fitar da kasafin sai da aka nemi Jin bahasin jama’a daga sassa daban-daban na shiyyar mazabar sanata uku da ake da su a jihar gami da neman masu ruwa da tsaki domin fitar da kasafin yadda ya kamatauma ya dace da muradu da bukatun jama’an jihar.
Gwamnan ya kuma bayyana cewar kasafin ya fi maida hankali kan sashin kiwon lafiya, noma, ilimi, da shimfida ayyuka. Daga nan ne ya nemi hadin guiwar Majalisar wajen hanzarin amincewa da kasafin domin bai wa gwamantin jihar zarafin cigaba da gudanar da ayyukan raya jihar.
Kazalika, ya gode wa mambobin majalisar bisa hadin kai da suke bai wa gwamnatinsa tun lokacin da suka dale karagar mulki inda ya misalta hakan a matsayin matakin bunkasa jihar.
Da yake maida nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Sulaiman ya ce za su yi duk mai yiyuwa wajen hanzarin bibiyar kasafin gami da amincewa da shi a kan lokaci.