Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Naira Biliyan 195 A Matsayin Kasafin 2022

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnatin Jihar Bauchi ta gabatar da naira biliyan N195,355,607,143:00 a matsayin kasafin kudin shekara ta 2022 da za a gudanar da manyan ayyuka da sauran fannin gudanar da ayyukan yau da gobe kamar yadda gwamnan Jihar Bala Muhammad ya sanar.

Wannan harsashen kasafin kudin ya kunshi naira biliyan N84,375,180,518 :00 kwatan-kwacin kashi 43 cikin dari da za a kashe wajen gudanar da ayyukan yau da kullum tare da ware naira biliyan N110,620,426,625 :00 kimanin kaso 57 cikin dari wajen gudanar da manyan ayyuka.

Da ya ke gabatar da kasafin a gaban kwaryar Majalisar dokoki jihar a Larabar nan gwamnan Jihar Bala Muhammad ya bayyana cewar wannan Kasafin na 2022 ya yi kasa da kaso 8.5 Idan aka kwakwanta da kasafin 2021 da muke ciki, a cewarsa rage kasafin ya faru ne domin su samu zarafi da damar fuskantar hakikanin halin da ake ciki domin tabbatar da karasa ayyuka ko cigaba da gudanar da ayyukan da suke akwai da wadanda ake son gudanarwa cikin nasara.

Ya kuma ce hakan zai basu damar dukkanin ayyukan da aka jero an samu damar gudanar da su a zahirance.
Daga bisani sai ya nemi hadin kan Majalisar dokoki jihar domin samun nasarar ayyukan da gwamnati ta sanya a gaba, ya kuma jinjina musu bisa goyon bayan da suka jima suna baiwa gwamnatinsa.

Da ya ke amsar kasafin, Shugaban Majalisar dokokin jihar, Abubakar Y. Sulaiman, ya bada tabbacin cewa kwamitocin da abun ya shafa za su yi hanzarin gudanar da ayyukan da suke gabansu domin ganin an samu yin aiki kan kasafin domin amincewa da shi don bada damar fara fara amfani da kasafin da wuri.

Exit mobile version