Khalid Idris Doya" />

Gwamnan Bauchi Ya Kaddamar Da Raba Tiraktoci Guda 500 Ga Manoman Jihar

A Talatar nan ne gwamnan jihar Bauchi Lauya Muhammad Abdullahi Abubakar ya kaddamar da fara raba Tiraktoci guda dari biyar (500), irin shuka, maganin feshi da sauran kayyakin aikin gona wanda gwamnatinsa ta APC ta samar domin rabawa ga manoma a farashi mai rahusa domin habaka sha’anin noma a fadin jihar.

Gwamnan ya kaddamar da fara rabon ne farfajiyar BSADP da ke Bauchi, inda ya bayyana cewar wannan yunkurin nasa na zuwa ne domin kyautata wa manoma sana’arsu, yana mai shaida cewar hakan zai habaka tattalin arzikin jihar gaya.

Da yake jawabi a wajen, gwamnan jihar Muhammad A. Abubakar ya shaida cewar wannan wani bari ne na cika alkawuran da gwamnatin APC ta yi wa jama’an jihar ta Bauchi.

Gwamnan ya bayyana cewar Tiraktoci guda 500 ne suka kaddamar da rabawa domin kyautata wa manoma sana’arsu, “Ababen da aka kaddamar sun hada da tiraktoci guda dari biyar wanda za a rarrabawa manya da kananan manoma; ina tabbatar muku cewa mun kirkiro wannan shiri na musamman tare da tallafin masana a wannan fannin na aikin noma na cikin gwamnati da ma na waje wadanda suka tallafa aka kirkiro da wannan shirin.

“Shi wannan shirin, ga duk wanda ya samu cin moriyarsa, yana dauke ne da rangwamen kashi 40 cikin 100 na kowace abar da mutum ya samu mallaka,” In ji Gwamnan Bauchi.

Gwamna Muhammad Abubakar ya kara da cewa, “A karon farko na wannan shirin mun yi yunkurin tallafa wa manoma dubu 40 a dukkanin fadin jihar Bauchi wadanda suka kunshi ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya, kungiyoyin kwadago makarantu na jihar da na kananan hukumomi; ababen da suka ci gajiyarsu sun kunsa maganin kwari da na ciyawa, kananan tiraktoci, abubuwan shuka na shinkafa, da abubuwan yanke shinkafar, abun yanke ciyawa a gonakai, hadi da abun tallafin kiwon kifi da matsar mai na gyada a dukkanin fadin jihar Bauchi,” In ji gwamnan.

M.A ya ci gaba da bayyana cewar noma tushen arziki ne, don haka ya himmatu domin kyautata wannan fannin a jihar Bauchi, “Aikin gona shine ginshikin ci gaba, kuma shine muka sanya a gaba domin bunkasa arzikin jihar Bauchi, ganin cewar kashi 80 zuwa 85 na ‘yan jihar nan manoma ne.

“Kafin na zauna zan shaida wa ‘yan asalin jihar Bauchi cewar rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya,” A cewar shi.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Kwamishina a ma’aikatar gona da albarkatun kasa na jihar Bauchi Malam Yakuu Kirfi wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar Dakta Bala Lukshi inda ya yaba gaya wa gwamnan jihar Bauchi a bisa gudunmawar da yake baiwa manoma a fadin jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewar ma’aikatansa a shirye suke a kowani lokaci da bayar da gudunmawarsu domin bunkasa harkar gona da kyautata wa manoma a jihar Bauchi.

Da yake jawabin godiya a madadin wadanda suka ci gajiyar shirin, Babban Limamin Bauchi Malam Bala Baban Inna ya gode wa gwamnatin kan hakan; yana mai addu’ar Allah baiwa gwamnatin damar ci gaba da habaka wa manoma rayuwarsu a kowani lokaci, ya bayyana cewar wannan yunkurin zai taimaki jihar Bauchi sosai.

Wakilinmu ya shaida mana cewar gwamnan ya kaddamar da rarraba tiraktocin wanda ake kiransu Tan-Tan, manya da kuma kananansu, hadi da irin shuka, takin zamani, maganin kashe kwari da sauransu.

Sai dai wakilinmu ya bayyana mana cewar Tiraktoci guda 40 ne suka bayyana a wajen rabon, inda ake sa ran ci gaba da kawo sauran wanda adadinsu zai kai dari biyar din da gwamnan ya kaddamar a wannan ranar, tuni dai aka fara raba wa wadanda suka ci gajiyar shirin kan rahusa mai sauki.

Exit mobile version