Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Mutfwang, a cikin wata takardar sanarwa da ofishin yaɗa labarai da harkokin jama’a na Gwamnatin Jihar Filato, Mista Gyang Bere, ya bayyana wannan jita-jita a matsayin aikin masu sha’awar raba kan al’umma da kuma waɗanda ke son kawo ruɗani kan kishin siyasar sa da kuma sadaukarwarsa ga jam’iyyar PDP.
- Kwamitin Amintattun PDP Ya Dage Kan Mika Shugabancin Jam’iyyar Ga Sashin Arewa Ta Tsakiya
- Kwamitin Amintattun PDP Ya Dage Kan Mika Shugabancin Jam’iyyar Ga Sashin Arewa Ta Tsakiya
Gwamnan ya musanta labaran da aka yi wa kwaskwarima da na’urar Kwamputa da ke nuna hoton sa tare da gwamnonin APC, yana mai bayyana hakan a matsayin wani shiri na ƙirƙirar rashin fahimta da kuma zargin sa da rashin amana.