ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kwamitin Amintattun PDP Ya Dage Kan Mika Shugabancin Jam’iyyar Ga Sashin Arewa Ta Tsakiya

by Yusuf Shuaibu
2 years ago
PDP

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya yi kira ga masu ruwa da tsaki daga shiyyar arewa ta tsakiya da su gaggauta fitar da sabon shugaban jam’iyyar na kasa domin maye gurbin Sanata Iyorchia Ayu.

An cimma matsayar ne a taron da ya gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja a wani gagarumin yunkuri na mayar da babbar jam’iyyar adawa ta koma kan turba.

  • An Samu Rarrabuwa Kan Yunƙurin Barin Damagum A Matsayin Shugaban PDP Har Zuwa 2025
  • ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP

Wannan kudiri wanda yana cikin jerin umarnin da aka fitar yayin wani taron gaggawa ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan halin da jam’iyyar ke ciki.

ADVERTISEMENT

Da yake karanta sanarwar, shugaban kwamitin amintattun PDP, Sanata Adolphus Wabara ya bayyana matukar damuwarsa kan shugabannin jam’iyyar na rigingimun cikin gida da ake fama da su, da kuma jinkirin warware muhimman batutuwan jam’iyyar.

Kwamitin amintattun ya bayyana matukar damuwa game da halin da PDP ke ciki, musamman game da tsarin gudanarwa da yanke shawara na kwamitin zartarwa na jam’iyyar. Ya bukaci kwamitin zartarwa da ya gaggauta daukar matakin maido da jituwa cikin gida, hadin kai, da amincewar jama’a ta hanyar bin kundin tsarin mulkin PDP, gami da bin tsarin karba-karba na mukaman jam’iyyaar ga dukkan sassan kasar nan.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

“Muna bukatar kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP ya mutunta tsarin mulki da ka’idojin jam’iyyar, wadanda suka kasance ginshikin nasararmu a baya,” in ji sanarwar kwamitin amintattu.

Kwamitin amintattu ya kuma yi Allah wadai da dage taron kwamitin zartarwa na kasa da aka yi, inda ya bayyana shi a matsayin cin amana a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Kwamitin ya dage cewa taron kwamitin zartarwar wanda yanzu aka shirya yi a watan Fabrairun 2025, yana mai gargadin cewa duk wani karin dage taron zai iya kara tsananta kalubalen da ake da shi da kuma haifar da yamutsi ga jam’iyyarmu.”

“Dole ne kwamitin zartarwar ya nuna shugabanci na gari ta hanyar kiran wannan muhimmin taro kamar yadda aka tsara. Ba wai kawai cika alkawari ba ne, har ma da matakin da ya dace don warware matsalolin da ke damun jama’a da kuma tsara kyakkyawar turba ga PDP,” in ji kwamitin amintattu.

Babban abin da ya fi daukar hankali a cikin kudirorin kwamitin amintattu shi ne, umarnin da ya bayar ga masu ruwa da tsaki a yankin arewa ta tsakiya da su yi taro cikin gaggawa tare da gabatar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Iyorchia Ayu.

Ko da yake Ambasada Iliya Damagun, ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yankin arewa, inda daga bisani ya zama shugaban riko na jam’iyyar na kasa bayan korar Ayu daga rugujewar shugabanci wanda ya kara dagula rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar.

Kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tanadi cewa a duk inda aka samu barin mukami a ofishin jam’iyya na kasa, sai wani daga shiyyar ya maye gurbin jami’in.

Da yake mayar da martani kan kudirin kwamitin amintattu, tsohon sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya yaba wa kwamitin bisa bai wa yankin arewa ta tsakiya umarnin gabatar da wanda zai maye gurbin Sanata Ayu.

Ya ce matakin ya yi daidai da bukatar shiyyar Arewa ta tsakiya wanda a ko da yaushe ke tada hankali kan cewa shugaban riko na kasa, Ambasada Umar Ilyasu Damagum ya koma kan mukamin da aka zaba na mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa tare da barin arewa ta tsakiya ta samar da magajin Ayu.

“Wannan matakin da kwamitin amintattu abun yaba ne sboda ya dace da matsayin jam’iyyar,” in ji tsohon sakatarenmai magana da yawun na jam’iyyar.

PDP
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ci-ma-zaunen Ƴan Siyasa Ne Ke Tunanin Yin Maguɗi A Zaɓen 2027 – Makarfi
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    An Samu Ruɗani Kan Rashin Bayyana Jerin Ƴan Takarar Jam’iyyun Siyasa Na Zaɓen 2027

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221
Labarai

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
Next Post
Shugabancin Nijeriya: ‘Yan Arewa Ku Jira Har Zuwa 2031 —Sakataren Gwamnatin Tarayya

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.