Khalid Idris Doya">

Gwamnan Gombe Ya Taya Zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi Murnar Lashe Zabe

Yayin Da A Ke Rantsar Da Su A Yau Litinin

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi 11 da mataimakansu tare da Kansiloli 114 murnar lashe zabe, yana mai kira a gare su da su dauki zaben su da aka yi a matsayin wata dama ta hidimta wa al’ummominsu, jihar da ma kasa.

A dai karshen mako ne aka gudanar da zaben kananan hukumomi na jihar wanda jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun kamar yadda hukumomin zabe suka shaida.

Bayan ayyana wadanda suka ci nasara a zaben da shugaban hukumar zabe ta jihar Gombe GOSIEC, Alhaji Sa’idu Shehu Awak ya yi ne kuma gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya taya jam’iyyar APC murna game da nasara da jam’iyyar ta samu a yayin zaben.

Gwamnan na taya jam’iyyar sa da ‘yan takararta murna ne ta cikin sanarwar da Ismaila Uba Misilli, babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai da hulda da ‘yan jaridu, Inuwa ya nuna farin cikinsa bisa gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare wani tashin hankali ba.

Inuwa ya kuma bayyana gamsuwar sa na yadda zaben ya gudana cikin nasara kuma lami lafiya kafin dama bayan zaben, yana mai cewa, “na ji dadi da yadda masu kada kuri’a da ma’aikatan zabe da masu sanya idanu suka gudanar  lamuran zaben cikin kwanciyar hankali.”

Sai ya taya wadanda aka zaba murna inda ya ce “ku dauki wannan nasara a matsayin damace da kuka samu don ku hidimtawa al’umma, ku yi iya kokarin ku don cimma kwarin gwiwa da ake da shi akan ku.”

Gwamna Inuwa Yahaya wanda jaddada muhimmancin kananan hukumomi sannan ya bukaci zababbun shugabannin da su aiwatar da shugabanci na gari da zai kai ga bunkasa rayuwar al’umma, karkashin kudirin gwamnatin jam’iyyar APC a jihar Gombe.

Idan za a iya tunawa, hukumar zabe ta jihar Gombe ta sanar da nasarar jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomi a dukkanin matakai kama daga Shugabanni 11 da Kansiloli 114.

A wani mataki makamancin wannan, Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da cewa a yau Litinin za ta rantsar da sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 11 inda su kuma za su rantsar da mataimakansu da kansilolin da suke karkashin kowace karamar.

A sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar Ibrahim Abubakar Njodi ya fitar, ya sanar da cewa gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya zai rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomin.

Ya ce, bikin rantsarwar zai gudana ne da karfe 9 na safiya a dakin taro na gidan Gwamnatin. Ya umarci a bi matakin kariya daga Korona yayin taron rantsuwar.

 

Exit mobile version