Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana kaduwarsa dangane da rasuwar Alhaji Abdulmumini Musa (Yariman Kwami) wanda ya rasu jiya Talata a Gombe.
Ta cikin wata sanarwar dauke da sanya hannun Kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, Gwamnan ya bayyana rasuwar shugaban na al’umma kuma mai rike da sarautar Gargajiya, a matsayin babban rashi ba ga iyalan sa ba kadai har ma ga daukacin jihar baki daya.
Sai ya mika ta’aziyyar sa ga daukacin al’ummar karamar hukumar Kwami bisa wannan babban rashi da aka yi, ya na mai addu’ar Allah Ta’ala ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa.
Hakazalika, gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar karamar hukumar Yamaltu Deba bisa rasuwar Alhaji Idi Baba Deba (Dan Rimin Deba) wanda ya rasu ranar Litinin a Gombe.
Sai ya yi addu’ar Allah ya ma sa rahama ya sa Aljanna Firdausi ce makomar sa, ya kuma bai wa wadanda ya bari a ba ya hakurin jure rashi, tare kuma da fatan Allah albarkacin bayan mamatan.