Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓensa a matsayin koma baya na wucin-gadi, wanda ba zai hana shi mayar da jihar kan turbar hadin kai da zaman lafiya da ci gaba ba.
BBC Hausa ta rawaito Gwamnan ya bayyana ƙwarin guiwar cewa za a dawo da nasarar da al’ummar jihar suka ba shi, domin ya umurci tawagarsa ta lauyoyi su shigar da ƙara a kotun ƙoli.
- Da Dumi-dumi: Kotu Ta Kwace Kujerar Gwamnan Filato
- Zanga-zanga Ta Barke A Filato Kan Kwace Kujerar Gwamna Mutfwang
Mutfwang, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya buƙaci al’ummar jihar da magoya bayan jam’iyyar PDP da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba su tabbacin za a martaba da kare zaɓin al’umma.
Ya kara jaddada aniyarsa ta bin doka da oda, ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za a cimma haske a karshe, domin ya yi imani da adalcin ɓangaren shari’a da kuma kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Mutfwang ya buƙaci magoya bayansa, da kuma ‘yan jihar da su tabbatar da doka da oda.
Ya kuma tabbatar da cewa jihar za ta yi nasara inda ya sake tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da yi wa jihar hidima da kwazo da gaskiya.