Daga Idris Aliyu Daudawa,
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ba da umarnin na a dakatar da Hakimai da kuma Magaddai a masarautar Maradun indsa aka kasha wasu Fulani cikin ruwan sanyi ranar Alhamis.
Gwamnan ya bada shi umarnin ne a lokacin da aka tarurrukan da suka shafi tsaro tare da masu sarautyar gargajiya, jami’an tsaro, shugabannin addini, da kuma ‘yan jarida, a gidan gwamnati dake Gusau ranar Alhamis.
Ya yi bayanin lokacin da ake taron cewar ‘’Abin bakin ciki ne daidai lokacin da muke shi wannan taron mun samu labaran da suka shafi tsaro guda biyu, daga kuma wurare daban- daban.
Ya ja kunnen mutane cewar daga yanzu duk wani mai sarautar gargajiyawanda aka samu wata matsala daga wurin da yake mulki, ‘Yan sa kai su kai mma wani hari, ko dai da kansu, ko kuma su dauki doka a hannunsu, mai bada shawara na musamman kada ya yi wani bata lokaci ya dakatar da shi, kafin a kafa kwamitin yin bincike akan shi al’amarin.
“Na samu labarin cewar na sai ma ‘yan ta’adda wadanda suka tuba mota kirar Hilud al’amarin da ba gaskiya bane saboda kuwa ban saya ba.
Ya cigaba da yin bayanin inda ya ce “Birgediya janar ko na taba ba wani dan ta’adda wanda ya tuba mota a wannan jihar? Gwamnan Zamfara ne ya tambayi Kwamanda Birget ta sojoji ta daya wadda ke Gusau.
Sai shi jami’in soja ya sanar da taron cewar sojoji a jihar har ma da shi kan shi, abin ma ya basu mamaki lokacin da suka ga shi rahoton, saboda kuwa shi gwamnan bai taba yin abu mai kama da wannan ba, in banda motoci 200 na aiki wadanda aka rarrabawa rundunonin tsaro shekarar data gabata.
Manema labarai sun bada rahoton cewar ba tare da bata lokaci ba sai gwamnan ya kira taron masu ruwa da tsakai akan shi al’amarin, bayan ya dawo daga aiki wanda ya sa ya bar jihar, wannan kuwa ya biyo bayan matsalar ‘yan ta’adda da kuma cece- kucen da ake ta yadawa.