Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamiti mai ƙarfi domin bincikar rahotannin da ke nuna cewa ana rage wa wasu ma’aikatan gwamnati albashi ko kuma ba a biyansu gaba ɗaya. Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin cin zarafi da take haƙƙoƙin ma’aikata, yana mai jaddada cewa ba zai amince da irin wannan dabi’a ba.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis ta ce an ba kwamitin wa’adin kwanaki bakwai domin yin cikakken bincike kan albashin ma’aikata daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025
- Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno
- Gwamna Lawal Ya Amince Da Ƙarin Albashin Wata Ɗaya Ga Ma’aikatan Zamfara
Za a gano yawan ma’aikatan da matsalar ta shafa, da binciko tushen matsalar, da kuma ba da shawarwari kan matakan da za a ɗauka don magance ta.
Kwamitin na ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan raya karkara da ci gaban Al’umma, Hon. Abdulkadir Abdussalam, wanda shi ne tsohon Akanta Janar na Jihar Kano. Akwai kuma kwararru a fannin kuɗi da tsarin biyan albashi a cikin kwamitin, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa ma’aikatan jihar cewa gwamnatinsa zai tabbatar da adalci da biyan albashi akan kari, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin lamarin. Ya ce wannan bincikeyana da nufin magance matsalar albashi da dawo da amincewa da tsarin biyan albashin ma’aikata a Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp