Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak of Kwara ya rushe dukkanin mambobin majalisar zartaswar jihar wanda ya fara aiki daga ranar 31 ga watan Disamban 2020.
Bayanin sallamar mambobin majalisar zartaswa na jihar na kunshe ne ta cikin kwafin sanarwar da Babban sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye wanda ya fitar a jiya Litinin a Illorin.
Sanarwar ta ce, sakataren gwamnan jihar Farfesa Mamman Jubril ne kawai ya tsira daga wannan dakatarwar inda har yanzu yake kan kujerarsa daram-dam.
Idan za ku iya tunawa dai, mambobin majalisar zartaswa na jihar su 16 gwamna AbdulRazak ya kaddamar da su ne a ranar 14 ga watan Disamban 2019.
Sanarwar ta ce, gwamnan ya kuma gode tare da yaba wa kwamishinonin nasa da ya dakatar bisa gudunmawar da suka bayar wajen cigaban jihar, ya na mai musu fatan alkairi a rayuwarsu na gaba.
Har-ila-yau, gwamnan ya sake cewa har yanzu sakataren gwamnatin jihar (SSG), Farfesa Mamman Sabah Jibril na kan kujerarsa daram-dam.
Gwamnan na Kwara ya kuma umarci tsoffin kwamishinonin da suka mika ragamar mulki ga manyan jami’an ma’aikatunsu nan take.