Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya isa jihar Borno tare da tawaga domin jajantawa Gwamna Umar Zulum da al’umman jihar Borno dangane da kisan gillar da yan Boko Haram sukayiwa Manoma 110 a makon da ya gabata.
Tawagar Gwamna Abdullah Sule da ta hada da Sanata Umar Tanko Al-makura da Tshon Sanata Danboyi da Sarkin Lafia da Sarkin Keffi.
Sun sauka a garin Maiduguri ne a yammacin ranar Asabar, Gwamna Abdullah Sule yace tawagar ta zone domin jajantawa Gwamna Umar Babagana Zulum da al’umman jihar Borno dangane da abin bakin ciki na kisan gillar da akayiwa manoma.
Gwamnan yayi kira ga al’umman jihar Borno da kasa baki daya da su kasance masu yin adu’o’in Allah ya kawo karshen wannan bala’in da gaggawa.
Gwamnan yayi kira ga Gwamnatin tarayya data ta kara jami’an tsaro a wannan yankin domin tabbatar da zaman lafiya ga al’umman dake rayuwa a yankin.
Gwamnan ya kara da cewa al’umman jihar Nasarawa suna kara jajantawa al’umman jihar Borno kan kashe kashen da akeyi a jihar.