Daga Muhammad Awwal Umar,
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya nemi jami’an tsaro da su bullo da wani sabon yaki da ‘yan bindiga kar su janye daga yankunan da abin ya shafa. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata takarda da aka raba wa manema labarai inda ya nuna takaicinsa ga wannan sabon harin ‘yan bindigar, inda suka kashe jami’an soja da dan sanda a kokarinsu na kawo zaman lafiya da kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Gwamnan ya bai wa al’ummomin Bassa da Zumba da wasu yankunan kananan hukumomin Shiroro da Munya da abin ya shafa a jihar tabbacin samar da rundunar tsaron hadin guiwa da za su cigaba da zama a wadannan yankunan don tsare rayuka da dukiyar jama’a.
Takardar manema labaran da gwamnatin jihar ta fitar, ta biyo bayan tserewar da mazauna yankunan ke yi ne bayan harin da ‘yan bindigar suka kai wa jami’an tsaro da ke zama a yankin, gami da watsewar da jami’an tsaron suka yi bayan harin matsugunnin jami’an tsaron da ke Allawa da ya kai ga rasa rayukan soja shida da dan sandan sintiri daya.
Gwamnan wanda ya nuna takaicinsa kan wannan harin da ya kai ga rasa rayukan, ya nemi mutanen yankunan da su kwantar da hankulansu, kuma ka da su bar mazaunansu, domin a cewarsa jami’an tsaron na shirya wani sabon tsari ne na yaki da ‘yan bindigar ba wai sun bar su ba ne gaba daya.
” Jami’an sojan sun kwashe gawarwakin gwarazan sojojin ne da suka rasa rayukan su a lokacin gumurzun, kuma yanzu haka suna cigaba da wani sabon shirin cigaba da aikin,” a cewarsa
Ya ce karuwar garkuwa da jama’a da hare-haren mahara a wasu sassan jihar, kira ne ga gwamnati a kan ta kara kaimi wajen bullo da sabbin tsare-tsare ga gwamnatin ta yadda jami’an tsaro za su samu kwarin gwiwar cigaba da ayyukansu, “ Ina ba da tabbacin za mu kawo karshen ‘yan ta’adda a jihar nan,” in ji gwamnan.
Ya kara cewa muna jajanta wa rundunar soja da ‘yan sanda da kuma al’ummomin da abin ya shafa na ayyukan maharan a kan rasa rayukan jami’an tsaron shida da sauran jama’ar da suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare a yankin.
Sakamakon ayyukan jami’an tsaron a yankin ya harzuka ayyukan maharan da ya kai su ga kai farmaki a matsugunnin jami’an tsaron da ke Allawa.
Rahotanni dai sun bayyana cewar a kallan maharan 200 ne suka kai farmaki a matsugunan jami’an tsaron inda suka kashe soja shida da jami’in dan sandan Mopol daya, tare fadawa cikin garin inda suka kashe mutum bakwai da yin garkuwa da jama’a da dama.