Gwamnan Yobe 2019: Hon. Sidi Yakubu Karasuwa Ne Zabinmu

Daga A.A.Kwaranga

Muna masu mika godiya ga Allah da ya ba mu Gwamna, Alh Ibrahim Geidam. Gwmna Geidam ka cancanci yabo, ubangiji Allah ya yi ma ka sakayya da abin da ya fi Alheri. Gwamna Alhaji Ibrahim Geidam, mu ba kungiyar Siyasa ba ce. Amma ya zama dole mu yi yabo ga babanmu Gwamna.

Kuma a tamu mahangar a siyasance, da kima muna rokon Gwamna Geidam da ya ba mu damar nuna namu dan takaran, wannan kuwa ba kowa ba ne illa Hon Sidi Yakubu Karasuwa saboda goyon bayan da ya bawa wannan jam’iyyar tun daga jiha har zuwa kasa baki daya.

A jamhuriya ta hudu da muka dawo kan siyasa, Hon Sidi Yakubu Karasuwa ya zama Shugaba Karamar Hukuma daga 1998 zuwa 2003, ya rike Shugaban jam’iyyar ANPP na Jihar Yobe daga 2004 zuwa 2007, shi ne kuma Sarkin yakin neman Zaben Marigayi Ssnata Mamman B. Ali a 2007. Haka kums ya zama Sarkin yakin Gwamna Ibrahim Geidam a 2011.

Hon. Sidi Yakubu Karasuwa ba a nan ya tsaya ba, ya sake jagorantar Sarki yakin Gwamna Alhaji Ibrahim Geidam a 2015 kuma duk Allah yana ba shi nasara. Wannan a fagen siyasa ke nan, banda mulki.

Da wannan dalili ne ya sa mu gamayyar matasan Sabuwar Nijeriya Reshen Jihar Yobe muke kira ga mai girma Gwamna da ya sa masa Albarka akan kiran da matasan Yobe suke yi ma sa.

Saboda mun fahimci akwai ‘yan siyasar da suka ci amanar talakawansu su ne suke yin biyayyar karya don a ba su dama su yi takara.

Saboda haka Muna kira ga mai girma Gwamna kar ya yarda da wannan tsarin.

‘Yan majalisu da Kwmishinonin da suka ci amanar talakawansu sun san ba za su samu kuri’a a wajen wakilan zaben ba, shi ne suke bin gari-gari don su yi amfani da yawun al-ummar Gwamna don ya ba su tsayawa takara kai tsaye, suna yin haka ne don sun ga Gwamna Geidam yana da kyakkyawar ala ka da talakawan jihar Yobe.

Don haka muna kira ga Gwamna da kar ya shiga wannan sha’anin nasu sabida shi ya gama lokacinsa lafiya zai dawo cikin talakawa ya zauna tare da mu kuma wasu sukeson su jawomar bakin jini a k krshen mulkinsa wanda kuma za su ci amanarshi daga karshe.

Muna son Mai girma Gwamna ya dube su daya bayan za, su waye ba su ci amanarsa ba ko ta iyayen gidansu a cikin masu kewaye-kewayennan?

Wassu mutane ne masu bin mulki akodayaushe. Yau in shi ma ya sauka, toh wanda ya hau shi ne nadu.

Dan haka muna rokon Gwmna da ya turosu wajen talakawa kowa halinsa ya karbeshi.

A.A Kwairanga, shi ne Shugaban tafiyar Hon Sidi Yakubu Karasuwa For Governorship 2019

Exit mobile version