Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya jajanta wa iyalan fararen hula da harin da jirgin saman Sojojin yaƙin ya rutsa da su a Tungar Kara da ke kananan hukumar Zurmi da Maradun.
Mataimakin na musammam kan yaɗa labarai da sadarwa na gwamna Suleman Bala Idris ne ya bayyana haka a takardar da ya sa mahannu ga manaima labarai.
- ‘Yan Bindiga Sun Yanka Wa Mutanen Zamfara Haraji Mai Yawa
- Zamfara Ta Shirya Wa Kiwo, In Ji Ministan Bunkasa Kiwon Dabbobi
A cewarsa harin ya rutsa da fararen hular da suka rasa rayukansu sakamakon ‘yan bindigar da suka tsere daga Gidan Makera a gundumar Boko a karamar hukumar Zurmi zuwa Kauyukan Maradun.
A cewarsa, rundunar Sojin Fansar Yamma da sauran Jami’an tsaron na iyalanka ƙoƙarinsu wajan yaƙi da ‘yan bindiga da suka addabi jihar.
“Wannan harin da sojoji suka yi ya rage wa ‘yan bindigan kwarin gwuiwa matuƙa, ya kuma nuna aniyar rundunar sojojin saman Najeriya na gudanar da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi na kare rayukan jama’a da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“A matsayinmu na gwamnati mai kishin kasa, muna tabbatar wa daukacin al’ummar jihar cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da dorewar nasarorin da aka samu a yaki da ‘yan Bindiga da. Nasarar da aka samu a baya-bayan nan na nuni da cewa kokarin hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na jiha da na tarayya ya haifar da sakamako mai kyau.
“A bisa wadannan nasarorin da aka samu, gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyar ta na bayar da dukkanin tallafin da ya kamata ga rundunar sojin saman Najeriya da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da gudanar da ayyukansu da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
“Gwamnatin jihar na mika ta’aziyyarta ga iyalan jami’an JTF da suka rasa rayukansu tare da ba su tabbacin cewa sadaukarwar da mamacin suka yi ba zai tafi a banza ba. Gwamnati za ta ba da tallafi da taimakon da ya dace ga iyalan wadanda suka rasu.
“A karshe, gwamnati na kira ga jama’a da su lura, su kai rahoton duk wani abu da ake zargi, sannan su ba jami’an tsaro cikakken hadin kai. ta hanyar hadin kai dan samun nasarar yaki da ‘yan Bindiga, tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.”