A ‘yan shekarun nan, idan aka tambayi wani mai sha’awar kallon fina-finan Hausa cewa, wane jarumi ne idan ya fito a matsayin mara tausayi abin ya fi dacewa da shi a Masana’antar Kannywood? nan take zai ce; Abubakar Waziri ko Baban Ma’u.
Asalin sunan Abubakar Waziri, Garba Muhammad; haifaffen Samaru a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Waziri ya bayyana da kansa cewa, shi mazaunin babban birnin tarayya; Abuja ne. Wata rana masu shirya fina-finai, sun tafi Abuja xaukar wani shirin fim; sai suka buƙaci ya fito a matsayin xan cikon benci a shirin nasu.
- Ba A Kowane Irin Matsayi Zan Iya Fitowa A Cikin Shirin Fim Ba – Isa Bello Ja
- Jariri Ya Yi Batan Dabo A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Kano
Haka kuwa aka yi, Waziri ya fara a matsayin xan cikon benci, bayan rawar da ya taka a wannan shirin; sai masu shirya fina-finan suka gano akwai baiwar da ke tattare da shi a harkar ta fim, sai suka ci gaba da ba shi ayyuka, in ji shi.
Zuwa yanzu, jarumin ya fito a cikin manyan fina-finan da suka samu tagomashin masu kallo a Masana’antar Kannywood, daga cikinsu akwai; Allah Ya Hana Babu, Kisan Gilla, Labarina, Garwashi da kuma Manyan Mata, wanda dukkanninsu ya taka rawar gani a ciki; ta hanyar fitowa a matsayin wani mara imani ko rashin tausayi.
Dangane da yadda mutane ke xaukarsa a matsayin mugu a zahiri, Waziri ya ce ko alama shi ba mugun mutum ba ne, kawai dai aikinsa ne a haka kuma dole ya zage damtse wajen yin aiki tukuru a duk lokacin da ya samu kansa a cikin shirin fim.
Ya ƙara da cewa; “Wani lokaci, na tava haxuwa da wani mutum; sai ya buxa baki ya ce, Allah ya tsine maka albarka; sai na ce da shi malam, wannan magana taka ta yi tsauri sosai; domin kuwa ya kamata ka san cewa, yadda nake a fim ba haka nake a zahiri ba. Kazalika, yarana sun tava dawowa daga makaranta suka ce ana ce musu ‘ya’yan mugu; sai na ce musu kada ku damu da maganganun mutane, ku kyale su kawai.”