Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya karyata labarin cewa ya kashe sama da Naira miliyan 400 a tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Wata jarida a Intanet ta ruwaito cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe Naira 170,276,294.31 wajen tafiye-tafiye na kasa da kasa, sai kuma Naira 221,567,094 na tafiye-tafiyen cikin gida sai kuma Naira 6,929,500.00 da suka shafi tafiye-tafiyen game harkokin tsaro cikin watanni uku.
- Li Qiang Ya Halarci Taron Shugabannin G20 Da Aka Gudanar Ta Kafar Bidiyo
- Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Inuwa
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce wasu bata gari ne suka kirkiri labarin da gangan domin su bata sunan gwamnatin.
Ya bayyana cewa wannan ya samo asali ne daga kuskuren fassarar bayanan kasafin kudin jihar, inda ya kara da cewa kashi na daya da na biyu da na uku sun fada karkashin gwamnatin da ta shude.
Sanarwar ta kara da cewa: “Mun karanta wani rahoto da ke zargin Gwamna Dauda Lawal na kashe sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Wannan karya ce kuma yunkurin bata sunan gwamna ne.
“Bin gaskiya da rikon amana su ne ginshikin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal. Ana iya samun dukkan bayanan da suka dace game da gwamnatin Jihar Zamfara a shafin zamfara.gov.ng.
Sanarwar ta ce: “Rahoton ya yi kuskure wajen danganta kudaden da gwamnatin da ta gabata ta kashe da kashe kudaden da gwamnatinmu ta kashe. Gwamnatinmu ba ta taba daukar jami’an tsaro masu zaman kansu aiki ba. Don haka, muna mamakin yadda aka dangana mana kudaden da aka kashe a watan azumin ramadan da kuma kudaden bikin sallah.
“A matsayinmu na gwamnati, mun himmatu wajen tabbatar da gaskiya a duka ayyukanmu. Mun yi wa al’ummar Jihar Zamfara alkawarin kawo sauyi mai kyau, kuma mun kuduri aniyar cika wannan alkawari.”