Gwamnan Zulum Ya Dauki Nauyin Karatun Jami’a Na Mutum 6,000 ‘Yan Asalin Jihar Borno

Sabon gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya dauki nauyin karatun Jami’a na mutum dubu shida ga ‘yan asalin jihar. Gwamnan ya dauki nauyin wadannan dalibai ‘yan asalin jihar a Jami’a mallakin jihar Borno (BSU).

Zulum ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai wa jami’ar a yau Lahadi a garin Maiduguri. Ya tabbatar da cewa dalibai 100 za a ba su damar karatun share fagen shiga Jami’a daga dukkanin kananan hukumomin jihar domin karantar bangaren kimiyyah.

Sannan a cewar gwamnan, za su dibi dalibai dari daga kowacce karamar hukumar 27 da ake da su a fadin jihar, tare da diban wadansu daliban 200 daga cikin garin Maiduguri da Jere baki daya.

Ya tabbatar da cewa bayan kammala horas da sabbin shiga, da bayan kammala karatunsu, za a bai wa mutum dubu uku koyarwa a manyan makaratun jihar. A yayin da ya ce; sauran dubu ukun za a ba su ayyukan yi a bangaren aikin soji da sauran Bangaren tsaro bayan sun kammala karatunsu a bangaren kimiyyar zamantakewa.

Wannan dawainiyyar karatun na su, ya hada da; dukkanin kudin makaranta, wurin zama da sauran su, tun daga kan karatun sharar fage zuwa digirin farko.

Gwamnan ya ce akwai shirin da suke yi na fara karantar da ilimin Likitanci a jami’ar jihar ta Borno nan da shekarar 2030.

Exit mobile version