Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya amince da gina babbar tashar mota a garin Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara a ɓangare aikin sabunta birnin jihar Zamfara.
Dauda ya bayyana haka ne a yau yayin taron majalisar zartarwar da ya jagoranta a gidan gwamnati dake Gusau.
Mataimaki na musamman ga gwamna Dauda Lawal a kan harkokin yaɗa labarai da Sadarwa, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana haka a wata takardar da ke ɗauke da sa hannun shi a Gusau.
- Cika Shekaru 161: Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Tallafawa Marayu 400 A Zamfara
- Gwamnan Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙirƙiro Ayyukan Ci Gaba
A cewarsa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina tashar Motar a kan kuɗi Naira Biliyan ₦4,854,135,954.53b.
Ginin Tashar Motar Wani ɓangare ne na shirin sabunta biranen jihar kuma zai inganta hanyoyin sufuri da samar da kuɗin shiga a jihar.
Ma’aikatar kula da kananan hukumomi da ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da yawon buɗe ido za su dauki nauyin aikin. Kuma ma’aikatar ayyuka da samar da ababen more rayuwa ce za ta sa ido a kan yadda za a gudanar da aikin.
Tuni ma’aikatar ayyuka ta tsara tare da samar da wani ƙudiri na cikin gida don gudanar da aikin tare da miƙa shi ga ofishin kula da harkokin ƙasa da ƙasa na jihar.
Babban filin ajiye motoci na zamanin ya ƙunshi abubuwa kama ofisoshin gwamnati da ƙungiyoyi, da Ofishin kashe gobara, da masaukin baƙi, da Asibiti, da Ofishin ƴan sanda, da ɗakin ajiya, shigar da cibiyar POS, da kafa cibiyar injina da wankin mota.