Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudirin ta na kare ‘yancin faɗin albarkacin baki, ƙarfafa adawa mai amfani, da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan jarida a Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da ake ci gaba da Zauren Bayani na Ministoci da ake gudanarwa a Abuja.
- Zargin Kisan Kiristoci A Nijeriya: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
Ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen kare ‘yanci da kundin tsarin mulki ya tanada, tare da ƙarfafa mahawara mai amfani domin inganta dimokiraɗiyya.
Ya ce: “Ina so in sake nanata cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yake cikakken ɗan dimokiraɗiyya, yana da niyyar kare ‘yancin ‘yan Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Haka zalika, yana ƙarfafa sukar gwamnati mai ma’ana da adawa tagari saboda suna da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen ingantawa da zurfafa tsarin dimokiraɗiyyar mu.
“Ina kuma tabbatar da cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida da samar da yanayi mai kyau ga aikin jarida a Nijeriya. Gwamnatin nan tana da yaƙinin cewa ‘yancin ‘yan jarida yana da muhimmanci wajen inganta nagartar shugabanci, gaskiya, da ci gaban ƙasa.”
Ministan ya yi amfani da damar taron don taya Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) murnar cika shekaru 70, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin wata babbar alama ta jajircewar su wajen kare ‘yancin ‘yan jarida da inganta aikin jarida.
Ya ce: “Ina kuma so in gode wa kafafen yaɗa labarai saboda jajircewar su wajen yaɗa muhimman batutuwan gwamnati. Wannan taro yana gudana a cikin wani lokaci mai muhimmanci, yayin da Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) take bikin cika shekaru 70. Wannan babbar alama ce da ke nuna yadda NUJ ke ci gaba da jajircewa kan ‘yancin ‘yan jarida da ingancin aikin jarida.”
Idris ya bayyana cewa Zauren Taron Bayani na Ministoci da ma’aikatar sa take jagoranta yana da manufar bai wa ‘yan Nijeriya damar samun cikakken bayani kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati, tare da jaddada ƙudirin gwamnati na nuna gaskiya da ɗaukar alhakin ayyukan ta.
“Wannan taro wata babbar dama ce ga ministoci su sanar da ‘yan Nijeriya irin cigaban da aka samu a ma’aikatun su. Ta wannan zauren tattaunawar, wanda aka inganta ta hanyar fasahohin zamani, muna tabbatar da ƙudirin mu na bayyana gaskiya da bayar da bayanai kai-tsaye dangane da manufofi, shirye-shirye, da sauye-sauyen da ke faruwa a ma’aikatun gwamnati.”
Ministan ya yaba wa Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, bisa ƙoƙarin sa na inganta martabar Nijeriya a idon duniya ta hanyar manufofin diflomasiyya da tsare-tsaren hulɗa da ƙasashen ƙetare.
Haka nan, ya jinjina wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, saboda irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa domin daidaita ma’aikatar daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp