Gwamnatin Tarayya ta shawarci dalibai mata dake makarantun sakandare da ke Abuja dasu rungumi ilimin kimiyya da fasa ganin cewa shikenan gaba za a dinga tunkaho da shi wajen gina kasa.
Darakta Janar na Hukumar Adana Bayanai da Inganta Kimiyya na kasa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya bada shawarar lokacin bikin ranar dalibai mata na ilimin kimiyya na shekarar 2017 da cibiyar IBI da kamfanin Beritav Solutions da kamfanin Media Range da kuma com.ng suka shirya a Abuja. Pantami wanda ya samu wakilcin Mataimakin Darakta na ilimin Kimiyya Injiniya Salisu Kaka, yayi nuni da cewa duk dalibar data rungumi ilimin na fasaha da kimiyya zai yi wuya ta rasa madafa a rayuwarta, kuma za su iya samun ayyuka a duk fadin duniyar nan.Ya ce,“idan kuka yi la’akari da kanan shekarunku, kun taki babbar sa’ana zamowa cikin fagen kimiyya a duniya.”
Shima a nashi jawabin Manajan kamfanin BeritadSolutions, Mista AyoOlagunju, ya bayyana cewa sun kaddamar da runbun tara bayanai inda zaa dinga ilimantar da jama’a akan ilimin kimiyya.