Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi
Gwamnan Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya bayyana yunƙurin gwamnatinsa kan bunƙasa harakar wasannin a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne kwanan nan a Birnin-Kebbi yayin da yake jawabi a wurin taron bikin bada kyautar wasannin guje-guje da ma’aikatar ilimi ta Jihar Kebbi ta shirya ga makarantun yankunan ilimi guda biyar na cikin jihar a ƙarƙashin jagoranci kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Muhammad Magawata Aliero.
Har ila yau, ya ce wannan tsarin da ma’aikatar ilimi ta Jihar Kebbi ta fito da shi wata hanya ce ta ƙara farfaɗo da harakar wasannin a jihar a tsakanin makarantun sakandare a duk faɗin jihar, tare da cewa yin hakan zai ƙara ɗaga martaba da darajar jihar kan harakar wasanni. Ya ci gaba da cewa jihar za ta shiga gasar guje-gujen da Jihar Legas ta shirya wanda za a gudanar nan ba da jimawa ba. Saboda haka ya ce, wannan shiri na ma’aikatar ilimi zai taimaka ainun ga shiga gasar Jihar Legas.
Yankunan da suka fafata a gasar sun haɗa da yankin Birnin-Kebbi, Yakin Bunza, Yankin Zuru, Yankin Yauri, Yankin Argungu da kuma Yankin Jega. Inda aka gudanar da guje-guje na mita 400 da mita 800 da mita 100 da kuma mita 1500 a tsakanin maza da mata.
Bayan kammala gasar, a gudun mita 400 na mata yankin Birnin-Kebbi ya zo na ɗaya, sai yankin Zuru na biyu da kuma yankin Bunza a matsayin na uku. Sannan
a gudun mita 400 na maza, yankin Argungu ya ciri tuta a matsayin na ɗaya, sai yankin Jega na biyu da kuma yankin Zuru a matsayin na uku.
A gudun mita 1500 na mata, yankin Birnin-Kebbi shi ne ya zo na ɗaya, sai yankin Zuru na biyu da kuma Yauri a matsayin na uku. A mita 1500 na maza kuwa, yankin Bunza ya yi na ɗaya, sai yankin Birnin-Kebbi na biyu da kuma yankin Zuru na uku. A gudun mita 800 kuwa, ɓangare maza yankin Argungu na ɗaya, yankin Jega na biyu, sanna yankin Bunza na uku.
A ƙarshe, Gwamnan Bagudu ya wasu kyaututtuka ga ‘yan wasan da suka yi nasara, haka shi ma kwamishinan kuɗi na jihar Alhaji Muhammad Ibrahim Augie, da mataimakin gwamnan jihar Samaila Yombe Dabai, sakataren gwamnatin jihar Alhaji Babale Umar Yauri , shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kebbi Barista Attahiru Maccido da kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Saminu Turaki.
A nasa jawabin, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Muhammad Magawata Aliero, ya yi godiya ga Gwamna Bagudu kan irin goyon bayan da yake bai wa ma’aikatar ilimi kan bunƙasa harakar ilimi a jihar da kuma muhinmanci da yake nuna wa kan harakar wasannin makarantun sakandare da kuma sauran muƙarraban gwamnatin jihar da ma’aikatan ma’aikatar ilimi da suka bada tasu gudunmawa waje tabbatar da wannan gasa gudana cikin nasara.