Bankin da ke bayar da lamunin gina gidaje na kasa wato FMBN, ya kirkiro da aikin gyaran ayyukan gidajen da aka yi wasti da su kimanin 46 a daukacin fadin Nijeriya.
Domin bankin ya cimma wannan kudurin na sa, ya yi hadaka da bankin bunkasa Afrika na gina gidaje wato (ADB).
- Bata Gari Sun Daka Wa Motar BUA Wawa A Kan Hanyar Zariya
- An Fara Gudun Yada-kanin-wani A Gasar Firimiya
Bankin na ADB dai, ya kasance wata cibiyar bayar da daukin kudade ne da ke bayar da goyon baya wajen gina rukunin gidaje a Afrika.
Manajin Darakta na banin FMBN Shehu Usman Osidi ne ya bayyana hakan a kwanan baya a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin mahukutan bankin na ADB.
A caewar Shehu, bankin na FMBN na bayar da fifiko wajen sake farfado da rukunin gidaje da ke a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa, bisa kara karfafa hadar zata taimaka wajen gina gidaje da kuma samar da rance ga masu gina rukunin gidaje a Nijeriya.
Shehu ya ci gaba da cewa, a Nijeriya a jihohi 36 akwai ayyukan gidaje sama da 46 da aka yi watsi da su, wadanda bankin na FMBN ya kudiri aniyar gyransu
Ya ci gaba da cewa,“Bincike ya nuna cewa, wasu bankuna sun kulla yarjajeniyar da jihohi yarjajeniyar domin bayar da kudade don gina gidaje, wanda ake sa ran jihohin za su samar da kayan aiki domin gina rukunin gidaje”.
Sai dai, Shehu ya ce, amma abun takaici akasarin jihohin sun gaza cika alkawuransu, wanda hakan ya janyo aka yi watsi da ayyukan na gina gidajen a jihohin su.
Shehu ya ce,“ Mun mun tuntubi bankin na ADB, wanda muka gano cewa, suna bayar da kudade, a saboda hana, mun shigo da su don su bayar da kudade don fara aikin farfado da ayyukan na gina gidajen don sayar da su ga ‘yan Nijeriya masu bukata”.
Ya kara da cewa, Nijeriya ce ta biyu da ke da hannun jari a bankin wanda ya kai kimanin kashi 15, wanda hakan zai bamu damar yin dubi kan yadda za a samar da kudade domin mu cimma burin mu na gina gidaje 100,000 ga ‘yan Nijeriya a 2024.
Ya ce, a yanzu bankin na FMBN na kan nazari kan yarjejeniyar da aka kaulla aka kuma yi watsi da ita kuma manufar ita ce domin amfanin ‘yan Nijeriya.
A na sa jawabin, shugaban bankin na ADB Thierno-Habib Hann ya ce, bankin na ADB ya zo Nijeriya ne wanzar da ajandarsa ta samar da kudaden bunkasa gidaje, wanda kuma ya gano cewa, Nijeriya masauki ce ta zuba jarin da ya kai sama da dala biliyan 25bn a duk shekara.
A cewarsa,“ A shirye muke mu yi hadaka da bankin FMBN da kuma sauran cibiyoyin da ke Nijeriya don mu cike gibin da ake da shi, na karancin gidaje, inda ya kara da cewa, kalubalem suna nan har da damar”.
A cikin wani kundin ta mika ragamar shugabanci da wakilinmu ya samu, tsohon Manajin Darakta na bankin FMBN Madu Hamman ya ce, shirin aikin gina giaje na NHF, bankin FMBN ne ya kirkiro da shi don ci gaba da gina gidaje a cikin saukin kudi ta hanyar zuba jari na dogon zango wanda za a rinka cire kashi 2.5, daga cikin albashin ma’aikata.
Madu ya kara da cewa, wasu daga cikin ci gaba da aka samu a watanni 12 da suka wuce a karo na farko a 2023, daukin kudaden da aka karbo sun dara Naira biliyan 100.