Gwamnatin Jihar Adamawa ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Lamurde bayan sabon rikicin kabilanci da ya sake kunno kai da yammacin Lahadi. Wannan umarni ya fara aiki nan take domin dakile yaduwar tashin hankali da kare rayuka da dukiyoyi.
A wata sanarwa daga Ofishin Mataimakin Gwamna, mai magana da yawun ofishin, Hussaini Hammangabdo, ya ce matakin ya zama dole ne bisa sabbin rikice-rikicen da aka samu a yankin. Ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya a Lamurde.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa
- Ku Je Ku Magance Matsalar Yunwa Da Ta Addabi Jama’a -Fintiri
Hukumar tsaro kuwa ta samu umarnin gaggawa domin shiga yankin tare da daukar matakai na dawo da doka da oda. An ce jami’an tsaro za su tabbatar da bin umarnin hana fita da kuma kiyaye duk wasu wurare masu hadari.
Gwamnatin jihar ta roki jama’a da su kasance masu bin doka tare da kiyaye zaman lafiya yayin da ake kokarin warware matsalar. Haka kuma gwamnatin ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan lamarin har sai an tabbatar da komai ya daidaita.














