Sama da naira biliyan dari biyu da sha uku (N213 billion) ne majalisar zartaswa ta jihar Bauchi ta amince da shi a matsayin kasafin kudi na badi wanda za a tura gaban majalisar dokokin jihar domin neman amincewarsu a kai.
Wannan bayanin ya fito ne ta bakin kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Bauchi, Dakta Aminu Hassan Gamawa yayin da ke ganawa da ‘yan jarida jim kadan bayan kammala ganawar mako-mako wanda gwamnan jihar ya jagoranta a ranar Talata.
Ya bayyana cewar kasafin an yi harsashensu ne ta hanyar samun kudi daga kudaden shiga na haraji da kason wata-wata da ake amsa daga gwamnatin tarayya gami da basukan da za a amso domin gudanar da ayyukan da aka tsara a cikin kasafin.
Kwamishinan ya shaida cewar da zarar majalisar jihar ta amince da wannan kasafin, gwamnan jihar Bala Muhammad zai samu dama da zarafin karasa manya da kananan ayyukan da ya ke kan gudanarwa a halin yanzu domin tabbatar da sun kammalu kamar yadda aka tsara don inganta rayuwar al’umman jihar.
Gamawa ya tabbatar da cewa kasafin 2021 zai taimaka matuwa wajen samar da wasu manyan ayyuka gami da tabbatar da jihar na biyan albashi, fansho da alawus-alawus a kan lokaci.
Ya kuma shaida cewar gwamnan zai gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar nan kusa domin tabbatar da neman amincewarsu a kai.
Har-ila-yau, kwamishinan muhalli da gidaje, Hamisu Muazu Shira, ya sanar da cewa za a kashe kimanin naira biliyan bakwai wajen gyarawa da kwaskwarima wa gidan gwamnatin jihar, masaukin gwamnati da ke Abuja da kuma samar da babban dakin taro na kasa da kasa a Bauchi.
Ya ce, daukan wannan matakin ya zama tilas ne lura da yadda gidan gwamnatin ya kasance an ginasa ne tun da jimawa da ke bukatar sabunta shi gami da zamanantar da shi.
Har-ilayau masaukin gwamnatin jihar da ke Abuja shi ma na matukar bukatar kwaskwarima da gyara lura da cigaban jihar.