Gwamna Borno, Babagana Zulum ya amince da kafa kwamiti mai mambobi 12 don aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bukar Tijani ya fitar a ranar Laraba a Maiduguri.
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Fannin Sabbin Makamashi Ya Samar Da Mafita Ta Tabbatar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Afirka
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 8 A Borno Da Yobe
A cewar sanarwar, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar, Babagana Mallumbe, shi ne shugaban kwamitin, yayin da shugaban ma’aikata, Mallam Fannami, ke matsayin mataimakin shugaba.
Haka kuma, an nada Babban Sakataren Ma’aikatar tsare-tsare, Sadiq Mohammed, a matsayin Sakataren kwamitin.
Sanarwar ta ce, ana sa ran kwamitin zai yi nazari a kan yadda za a daidaita mafi karancin albashi a jihar a Borno.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, akanta-janar, babban mai binciken kudi, da shugabanin NLC da TUC.